Darajar Mace Tana Da Girma Sosai...!!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


Allah maɗaukakin Sarki Ya faɗa a cikin Alƙur'ani mai girma "Allah bai ɗorawa kowacce rai ba face abinda zata iya"


Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya faɗa a cikin hadisi ingantacce "imanin ɗayan ku bazai cika ba har sai ya so wa ɗan uwansa abin da yake so wa kansa"


Da wannan nake son mata mu sani Allah Ya halicce mu da matuƙar daraja, sannan yayi mana sutura inda Allah Ya ƙaddara tsarin rayuwar mu a ƙarƙashin namiji.


Daga lokacin da aka haife ki har zuwa lokacin auren ki, kulawa da rayuwar ki ya rataya ne akan mahaifinki ko wani muharraminki (a yanayin da babu mahaifi).


Idan kikayi aure kuma sai wannan nauyin ya koma kan mijinki.


A yayin da girma ya kama ki ana fatan ragaramar kulawa da rayuwar ki ta koma hannun yaranki maza.


To a dalilin haka ya sa, a kowanne mataki na rayuwar ki ya kamata ki zama mai biyayya ga iyayenki da mijin ki sannan ki kare mutuncinki don ki zama abar alfahari ga yaranki.


Duk da haka Allah Ya jaddada nuna irin darajar da Yayi miki ta hanyar sanya ki a cikin kowace ibada da ɗa namiji zaiyi, hatta yaƙi Annabi (SAW) ya tafi da mata a lokacin sa.


Abinda nake so in nuna a nan shi ne, ƴar uwa ta duk abinda za kiyi a gidan auren ki kiyi don neman yardar Allah, kiyi saboda Allah Ya umarce ki da yin hakan.


Kowacce zuciya na san tana son a kyautata mata, tana son in tayi abun yabo a yaba mata. To amman sai ya zamana wasu mazan su ba haka suke ba, sunfi son a koda yaushe ke ki kasance mai kyautata musu ba tare da su sun kyautata miki ba, sannan basu iya yabo ba illa ma suna jiran laifi ƙalilan da zasu fara faɗa akai.


Saboda haka ƴar uwa duk wata biyayya da zaki wa mijin ki, ki masa tsakanin ki da Allah, kinga ko da bai yaba ba kin san ladan ki yana wurin Allah maɗaukakin Sarki.


Kar ki wa mijinki biyayya don neman tukuici, sai ki iya samun tukucin a nan duniya amman kuma baki da komai a lahira kinga anyi ba ayi ba kenan.


 Real Ameenah Muh'd

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post