'DAN NIGERIA:' Nadai Daga Cikin Halittu Da Allah (T) yayi Amma a 'Dabi'a ya fi kama da dabba, amma a wajen tunani Dabba ta fi shi....!!!



MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES  

WANENE 'DAN NIGERIA ???

'Dan Nigeria ta daga cikin halittun da Allah yayi, kuma ya sanya su mutane wadanda za su riqa mu'amala da kuma cudanya irin ta mutane.


Sai dai kuma a dabi'a ya fi kama da dabba, amma a tunani dabba ta fi shi.

Domin ita a kowanne irin hali ta kan bawa 'ya'yayenta kariya da kuma qin ganin an cutar da su.


   DAGA CIKIN 'DABI'UNSA

_____________________________________


(1)- Zai iya karo da dutse akan hanya, amma maimakon ya kawar da shi don ka da wasunsa su cutu sai ya bar shi a wajen.


(2)- Ba ya bin doka kowacce iri ce, amma shi yana so wani ya bi dokar da ya tsara.


(3)- Duk abinda zai sa mi dan'uwansa na cutarwa matuqar ba shi ta shafa ba, to ba ya damuwa.


(4)- Yana so ayi masa adalci, amma ba ya so a yiwa waninsa in akwai sabanin fahinta tsakaninsu.


(5)- Ba shi da 'yancin tunani, da za ka kira wani abu baqi da sunan fari, to shi ma fari fat ne a wajensa.

Misali:-


A tarihin Nigeria  ba a taba samun Azzalumi kamar Buhari ba, amma da aka samu wasu lalatattu su ka kira shi da mai adalci sai 'yan Nigeria su ka tafi akan cewa adali ne, ba tare da tunanin a ina adalcin nasa ya ke ba.


(6)- Zai iya daukar kwangilan kashe 'yan qasarsa kawai don neman biyan buqatun kansa.


(7)- Shine Wanda jama'a za su zabe shi bisa alqawuran da yayi musu, amma da zarar ya sami shugabanci sai ya manta dukkan alqawuran da ya dauka.


(8)- Shine ya dauki addini a matsayin kasuwanci (business) da kuma yayi, bai san addini neman yardar Allah ba ne.


(9)- Shine za ka iya ba shi amana, amma sai ya maida kayan tamkar mallakinsa.


(10)- Shine wanda bai dauki qarya abin kunya a idon duniya ba, ballantana ya san illarta wajen mahaliccinsa.


WADANNAN KADAN DAGA CIKIN HALAYYARSA KENAN.


Daga wakilanmu na Zone din Bauchi, Gombe da Adamawa


Tare da ( Ado Isah Guda )

08137925034/08126385470

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post