Inji Almajiran Shehin Malamin
Muna da dalilai da yawa da suka sa muka nemi Maulana Amerul Waizina Sheikh Abduljabbar ya bamu dama mu ɗaukaka ƙara.
1- Yadda Sheikh Abduljabbar yake da haƙƙi akanmu ( Ɗaliban sa) muma muna da haƙƙi akansa, kamar da Allah Ta'ala ya bayyana Haƙƙin Uba akan ƴaƴansa da Haƙƙin ƴaƴa akan ubansu.
Dan haka munyi Amfani da wannan Haƙƙin namu mun nema Daga gare shi kuma Alhamdulillahi ya sauke wannan Haƙƙin na mu.
2-Kotun Da ta yanke Hukuncin kisa Ga Maulana Amerul Waizina ba muji ta Karanto Aya ko Hadisi wajen Yanke Hukunci ba, Sai mukaji Ta Jawo Sakin Layi Wanda Wasu Mutane suka zauna Suka ƙirƙira.
Don haka muka zaɓi ɗaukaka ƙara inda ba za'a fake da Guzuma a harbi karsana ba, Ace Shari'ar Allah za'ai Alhalin Karya ne Shari'ar Da wasu suka tsara za'ai.
3- Maƙiyan Malam (H) masu son ganin bayan sa, sunyi Amfani da Hukuma da hanyoyi na zamani dan sheƙar da jininsa, saɓanin Yadda Magabatan da suka biyo wannan hanya ake sheƙar da jininsu ta hanyar fito na fito ko hanyar sunƙuru (Guba)
Dan haka muma muka nuna wa Duniya kan mu a waye yake Duk wata hanya da suka sani ta zamani da ake sheƙar da jini ko kare shi mun sani, dama tun farko mun zauna a wannan kotun ne dan wasu dalilai, Yanzu kuma za mu bi wannan hanyar Domin kwatar haƙƙinmu.
4- Ba za mu bari Burin wasu ƙaskantattun bayi ya cika ba, masu son ganin bayan Malam (H) Su babban burinsu a ce yau Malam Abduljabbar baya Duniya, Kuma Burin su ace Mutuwa yayi ta Wulaƙanci, mu kuma ba za mu bari Wannan Burin nasu ya cika ba, ko da agun mu muna Ganin Mutuwa a wannan harkar Mutuwa ce Ta izza da Ɗaukaka To gama Garin mutane ba haka zasu ɗauka ba, kuma hakan na iya jefasu Cikin duhun da Malam (H) yai shekaru yana son ya haska musu fitila.
5- Muna da burin Rahamar Allah ta mamaye dukkan Halittu, kuma munyi Raja'in Wannan Hanyar ( Ta Wilaya Ga Ahlilbaiti) itace Siraɗul Mustaqem, dan haka muke fatan kowa ya shiga Wannan Rahamar, ta hanyar Maulana Amerul Waizina ya dauko Fitilar Haska hanyar gadan gadan.
Kaɗan kenan daga dalilan da yasa muka nemi Ɗaukaka ƙara akan Hukuncin da Kotun.
@ Jawad Salisu Umar Gano
Mujamma'u Ashabilkahfi Warraqeem
17th December 2022