DALILIN DA YASA AKA RUFE SHEIKH ABDULJABBAR KABARA




Bai Yarda Iyayen Annabinmu Suna Wuta Ba, bai Yarda Abu Dalib Da Ya Taimaki Annabinmu Yana Wuta Ba.


Bai Yarda Mala'ika Ya Shaƙe Annabinmu Ba, Kuma bai Yarda Annabinmu Ya Rasa Hankalinsa Yayin Farai Masa Wahayi Ba


Bai Yarda Anyiwa Annabinmu Sihiri Ba, kuma bai Yarda Annabinmu Yana Ganin Wai Kamar Yana Zuwarwa Iyalansa Ba


Bai Yarda Annabinmu Yaje Gun Wani Bayahude Yana Neman Sanin Shi Waye Ba, Kuma Bai Yarda Annabinmu Ya Hau Kan Sama Da Niyar Ya Faɗo Ya Kashe Kansa Ba.


Bai Yarda Annabinmu Ya Zaga Matansa Gada Ɗaya A Dare Daya Ba, Kuma Bai Yarda Matansa Sunkai Kararsa Akan Yai Musu Adalci Tsakaninsu Ba.


Bai Yadda Annabinmu Yaga Wata Mata Ya Tafi Gida Ya Biya Buƙata Ba, Kuma Bai Yarda Wata Yazo Tace Ya Biya Mata Buƙata Ba.


Bai Yarda Annabinmu Yana Aika Ummu Sulaimun Ta Gano Masa Mataba, Kuma Bai Yarda Annabinmu Yana Kwantawa Akan Cinyar Matar Wani Ba.


Bai Yarda Annabinmu Yana Aure Bisa Tilas Ba, Kuma Bai Yarda Annabinmu Ya Tsuguna Wata Ta Taka Cinyarsa Ta Hau Doki Ba.


 Bai Yadda An Aiko Annabinmu Dan Yai Kashe Mutane Ba, Kuma bai Yarda Annabinmu Idan Yaje Gari Sai Sauraro Idan Yaji Ba'a Kira Sallah Ba Ya Afka Musu Ba.


Bai Yarda Annabinmu Yana Kyauta Ya Kwace Ba, Kuma Bai Yarda Annabinmu Yana Fitsari Akan Bola A Tsaye Ba.


Bai Yarda Wani Yana Bin Annabinmu Bandaki Ba, Kuma Bai Yarda Annabinmu Ya Buya A Bayan Wani Agun Yaƙi Ba.


Bai Yarda Annabinmu Ya Rasu Yana Kakari Ba, Kuma bai Yarda Annabinmu Ya Cika Yana Sambatu Ba.


Bai Yarda Da Duk Wani Hadisi Daya Taɓa Darajar Annabinmu Ba, bai Yarda Da Duk Wani Hadisi Da Yaci Karo Da Aya Ba

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post