Rahoto daga babban Masallacin juma’a na kasa dake Abuja, almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun fito gangamin kiran asaki Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara.
Yan uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun sabunta fitowa kiran a gaggauta baiwa Shaikh Zakzaky da matarsa fasfo dinsu domin su fita neman lafiya kasar waje, a yau juma’a ma masu gangami sun sake fitowa tare da kiran gwamnatin Kano da ta gaggauta sakin Sheikh Abduljabbar daga tsarewar zaluncin da take mishi.
Masu gangamin sun fito ne dauke da hotunan Shaikh Abduljabbar d’an marigayi ne babban Malamin darikar kadiriya wato Sheikh Nasiru Kabara, tare da gabatar da wakokin kira ga gwamnatin jihar Kano kan ta gaggauta sakin Sheikh Abduljabbar daga tsarewar zalunci da take mishi sama da shekara Daya.
-Asperger
-AliSajjadIbnTaheer
-Isa Charis
30-12-2022