Kabaru tayi watsi da sukar da lawyoyin Malam Abduljabbar sukayi akan ingancin tuhuma tun daga farkon shari'ar zuwa jawabin karshe da aka gabatar a rubuce.
2. Kotu ta gamsu cewa dukkan kalaman da ake zargin Malam Abduljabbar Kabara da furta su, shine ya kirkire su.
3. Kotu ta karbi shedun da masu gabatar da ƙara suka kawo gaban kotun.
4. Kotu tana ganin cewa, korewar da Malam Abduljabbar yayi ba za ta kubutar da shi daga hukuncin da doka ta tanada ba akan wanda ya furta kalaman ɓatanci ga Annabi SAWA.
5. Kotu ta yi watsi da duk wani bayanin da Malam Abduljabbar yayi wanda bai da alaka da tuhumar da ke gaban ta.
6. Kotu tace Malam Abduljabbar yana fassara kalmomi ba tare da la'akari da siyaƙin da maganar ta zo ba, kuma baya fito ma'ana kyakkyawa sai mummuna akan hadisai.
7. Kotu ta kore fassarorin da Malam Abduljabbar Kabara yayi, ta kuma bayyana cewa fassarorin da Farfesa Ahmad Murtala sune suka fi daidai da ma'anar hadisan, sannan kuma ta tabbatar da cewa ta karbi shi a matsayin kwararre a fannin hadisi.
8. Kotu tace bata gamsu Malam Abduljabbar Mujtahidi ne muɗlaki, kuma bata yarda da kwarewar sa ba.
9. Kotu tayi hukuncin cewa ta samu Abduljabbar Kabara da laifi kamar haka;
A. Ƙage wa maaikin Allah da jafa'i takan kirkira masa kalmar fyade don cin mutuncin ma'aiki SAWA wanda ya saba da sashe na 382 (b) sharia Penal Code.
B.Ƙage wa maaikin Allah da jafa'i takan kirkira masa kalmar kwace don cin mutuncin ma'aiki SAWA wanda ya saba da sashe na 382 (b) sharia Penal Code.
C. Ƙage wa maaikin Allah da jafa'i takan kirkira masa kalmar Auren dole don cin mutuncin ma'aiki SAWA wanda ya saba da sashe na 382 (b) sharia Penal Code.
D. Ƙage wa maaikin Allah da jafa'i takan kirkira masa kalmar Biyan bukata tsakanin namiji da mace don cin mutuncin ma'aiki SAWA wanda ya saba da sashe na 382 (b) sharia Penal Code.
10. Kotu ta bawa wanda yake riƙa wa lawyan dake kare wanda ake ƙara dama ko yana da wata magana. Lawyan yace yana rokon a sassauta wa wanda ake ƙara wajen hukunci kasancewar sa mai iyali, kuma magidanci, sannan kuma yayi maganganun da yayi ne bisa kuskure da rashin fahimta.
11. Malam Abduljabbar Kabara ya ce shi bai san wannan lawya ba, kuma ba wakiltar da yake ba, kuma ba da yawun sa yake magana ba, saidai kotu baya saurari wannan koke na Malam Abduljabbar ba , ta cigaba da sauraren rokon da lawyan yake yi a madadin Malam Abduljabbar Kabara.
13. Kotu ta ce ita ta gamsu wannan lawya wakiltar Malam Abduljabbar yake, domin wanda kotu ta wakilta ne ya aiko shi.
14. Malam Abduljabbar a jawabin sa na karshe yace bayan na saurari duk abinda ka fada na juya duk hujjoji na sama a ƙasa, ka ƙaga mun zagin Annabi SAWA... Anan ne lawyan masu gabatar da ƙara Shu'aibu Sa'idu SAN ya ce; "Wannan magana da yake ba magana ce da zai faɗi wannan maganganu a kotu ba. Ai damar da aka bashi, na ya nemi sassauci ne ba na mukabala a Shari'a ba, kuma ba lokaci ne na ya kalubalnci hukuncin da kotu tayi ba. Ina rokon kotu ta datse shi.''
15. Kotu tayi umarnin a bar Malamin ya cigaba da bayanin sa, ya cigaba da cewa;
''Ni bana neman sassauci akan wannan laifi da ban yi ba, ina bawa masoyana hakuri, kar su samu damuwa kan tafiya ta lahira, zanyi mutuwa ta girma, kuma bana neman kai Ibrahim Sarki kayi mun sassauci, kuma a gaggauta yi mun hukuncin nan. Kalami na na karshe kenan. '' inji Sheikh Abduljabbar.
Jarida Radio
15/12/22