Shahid Hammad Ibraheem Zakzaky H |
Cikakken Tarihin Shahid Hammad Ibraheem Zakzaky
Haihuwar Sa:
An haifi Sayyid Hammad Ibraheem Zakzaky ne a rana mai kamar ta 01 ga Sha'aban 1417 Hijira dai-dai da 10 Ga December 1996 Miladiyya. A cikin birnin Kadunan Tarayyar Nijeria.
Sunansa Da Laqabin Sa:
Sunan sa Sayyid Hammad Ibraheem a na yi masa laqabi da Sajid.
Nasabarsa Ta Wajan Uba:
Nasabarsa ta wajan mahaifin sa: Sayyid Hammad, shine dan Allamah Ibrahim Zakzaky, na 7, shi kuma dan Malam Yaqoub shi kuma dan Malam Aliy dan Malam Muhammad Tajuddin dan Liman Husaini. Shi Liman Husaini wani bawan Allah ne kuma babban Malami da take limanci a wani Masallaci a lokacin. Malam Muhammad Tajuddin ya zo birnin Zariya ne daga Sokoto a cikin tawagar Amir na Zariya. Wato lokacin da Shaikh Usman Dan Fodiyo (Ra) ya nada Malam Musa a matsayin Amir na Lardin Zazzau sai ya hada shi da Malam Muhammad Tajuddin a matsayin mai bashi shawara, da kuma mai taimaka masa wajan tafi da harkokin jama'a akan tsarin Musulunci.
Asalin iyayen su, sun fito ne daga Magarib, Maroko kenan a wancan lokakacin. Musamman ma daga wani birni da ake ce masa Shingidi, wanda yanzun yana cikin Muritaniya ne. Amma a lokacin babu Muritaniya, Shingidi ake ce masa. Kuma sun tashi daga sassa zuwa sassa har suka zauna a Mali ta da. Kuma daga can suka zo nan. (Nigeria). Ana cewa suna daga cikin 'sulala' (zuriya) din Imam Hasan Almujitaba (As), wadanda suka zauna a kasar Magarib. Daga nan suka gangaro su kai Mali, suka fado nan kasar Nigeriya.
Nasabar Sa Ta Wajan Uwa:
Sayyid Hammad dan Malama Zeenah ita kuma sunan maihaifinta Ibrahim sunan mahaifin shi Muhammad Auwal. Sunan mahaifiyar ta Maryam sunan mahaifin mamanta Abdullahi. Mahaifiyar ta Maryam ita jikanyar Imam Akayede ce wani babban Malami dake Illorin jihar Kwaran Taraiyyar Nijeriya.
Karatun Shaheed Hammad:
Sayyid Hammad ya fara karatun sa ne a gun mahaifiyar sa tun da shi ya taso ne mahaifin sa na tsare a kurkukun Abacha, ya yi karatu irin yanda aka saba kuma karatu mai zurfi a bangare Kur'ani Dmda sauran karatukan gida da ake cewa karatun littafi a cikin birnin Zariya.
A Bangaren Karatun Boko Kuwa:
Sayyid Hammad an ci gaba da koyar dashi a gida daga shekarar da aka haife shi watau 1996 Zuwa 1998. Bayan Wannan rainon sai aka sanya Shaheed makaranta a matakin raino, watau 'Day Care' ko kuma 'Kindergarten' daga shekara ta 1998 zuwa 2000 a makarantar 'Buks International School' dake a Kwangila daura da makarantar koyon tukin jirgin sama dake a Zariya, eatau 'Aviation'.
Daga gama wannan mataki sai aka sanya shi a matakin dake gaba da wannan watau mataki na 'Nursery School' a shekara ta 2001 zuwa 2003 duk a makarantar ta 'Books International School'. Bayan Shahid ya kammala wannan mataki sai aka sa shi a mataki na gaba watau mataki na 'Primary School' a makarantar 'Zaria Children School'. Shaheed ya yi wannan mataki a wannan makaranta daga shekara ta 2004 zuwa 2009.
Bayan kammala karatun sa a mataki na 'Parimary' sai ya tafi mataki na gaba watau mataki na karamar 'Secondary' daga shekara ta 2010 zuwa 2012 inda ya kammala aji na daya zuwa na uku a sashen 'Secondary School' dake a makarantar 'Zaria Children School'. Bayan kammalawa da karamar 'Secondary' sai ya jona da sashen babbar 'Secondary' dake a wannan makaranar daga shekara ta 2013 zuwa 2015.
Sayyid Hammad ya yi shahada ne a cikin gidan mahaifin sa Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) dake Unguwar Gyallesu sakamakon harin kisan kiyashin da sojojin Nijeriya suka kaiwa Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) da sunan wai almajiran sa sun tarewa shugaban sojoji hanyar wucewa a Husainiyya Baqiyyatullah dake da nisan kimanin kilomita 2 zuwa gidan shehin malamin dake Unguwar Gyallesu, Sayyid Hammad sojojin Nijeriya sun yi masa yankan rago da harsashi a wuyan sa a lokacin da ya ke bawa mahaifin sa Shaikh Zakzaky kariya daga harin zaluncin sojojin.
Amincin Allah ya tabbata a gare ka ya Shaheed Hammad, ranar haihuwar ka da ranar shahadar ka da ranar da za'a tasheka tare da madaukin fansar da ba'a nasara akan sa(AF)
✍️ Journalist
Dan Fudiyya
10/12/2022
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com