CIGABA KASHI NA : JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY YAYIN GANAWA DA 'YAN POLITICAL FORUM (5)

 



‘YAN KWAMASHIYAL SUNA SON YIN AMFANI DA SUNANMU


To sai naga cewa, bayan wadannan maganganun da su wadanda ake tare da su suke yi, sai ya zama kusan ma abin da wadanda muke cema ‘yan Kwamasiyal din nan suke yi suma shi suke yi. Domin su ‘yan kwamasiyal da suka yi ta kokarin su nuna tare suke da mu a sha’anin da ya shafi siyasa, su ne fa jiya suka yi ta jafa’i a kanmu, ba jafa’in da basu yi ba. Har yanzu kuma basu daina ba ma, da cin mutunci da cin zarafi. Aka basu Rediyo da Talabijin suka yi ta mana abubuwa, suka yi hira da gidajen radiyo suka farfada mana maganganu, lokacin sun dauka shikenan karshenmu ya zo, suka nuna ba wani abin da ya hada mu da su. 


To yanzu kuma wai yanzu mun hadu, wai yanzu sunanmu wai Duk Shi’a. Saboda mene? Allah Ta’ala ya hana su mutane, ya haramta musu. Don akwai wani lokaci da shi mai ba da shawara kan tsaro ya taba cewa to su wadannan Shu’a din da suke goyon bayan Buhari, a basu Eagle Square mana su yi ‘rally’. Sai wani yake ce masa ai da su da magoya bayansu duk ai basu wuce ka saka su a ‘luxury’ guda daya ba. Sai yace shine muka kashe wadannan kudin da yawa haka? 


Tunda yake an san inda jama’a suke, to yanzu sai a ci da sunan Shi’a. (Sai suka ce) Duk gaba daya Shi’a. Ko ba haka ba? Ya yi daidai. Sunanmu mene? Shi’a. (In abin a tambaye su) ku ne ‘yan gwagwarmayar nan da ba gudu ba ja da baya? (Sai su ce) Eh, mune mana. 


To a yanzu kam wannan yana yiwuwa. Amma da ya ji tatas (harbi), idan ya danna a guje sai kauyensu. Ya faru ne ai. Wasu sun ji na yi tas-tas, a kusa da su ne ma a unguwarsu, randa aka yid an tatatas din nan a sharada, wani da ya danna a guje sai kauyensu. Wani kuma ya je wani gida, yace ya je wajen guggunsa ne, ya shiga karkashin gado ya maqe. Duk ‘yan kwamashiyal din nan ne, da sun ji daram sai ka ga sun danna a guje. Ko da aka yi mana abin da aka mana suka yi ta jafa’i, amma yanzu sun zo wai sunanmu Shi’a. In bukatarsu ta biya suka samu abin da suka samu, to za su dawo kan nufinsu, ko yau kuma aka sake dira mana za su sake yin irin abin da suka yi jiya, ba makawa.


ABIN BAN-HAUSHI A TARON DA KUKA YI A SAKKWATO


To sai muka ga wannan abin sai ya zama abin da ya zama. Wani abin da ya fi ban-haushi ma shine taron da (ku ‘yan Political Forum) kuka yi na Sakkwato, da shima aka yi ta maganganu masu ban-al’ajabi, aka yi ta maganganu, maganganun marasa dadin ji.


Daga cikin maganganun da aka yi har da wanda yake cewa, wai in nan ce Malama (Zeenah) ta nuna rashin goyon bayanta ga wannan ai ba wani abu bane, saboda an kashe ‘ya’yanta ne. Yace wai shima akwai ‘yar uwarsa da aka kashe mata ‘ya’yanta hudu, wai ita ma da ta ji ance Political Forum, tace ya za a yi haka nan!


Wato kenan, idan aka kashe maka ‘ya’yanka baka gane kan-gadon abubuwa. Wato wanda ba a kashe musu ‘ya’ya ba sun fi kan-gado, -sun fi gane abin da ya kamata. Kamar Ummul Banin (SA) kila ba za ta gane cewa bai kamata a sasanta da Yazidu ba, kila wanda ba a kashe masa kowa bay a fi ta hankali. 


Haka ma Sayyida Zainabul Kubra (SA) tunda an kashe mata ‘ya’yanta, ita ma kila za ta ga bai kamata a sasanta da Yazidu ba, amma su wadanda suka da hankali, masu wayewa, za su ga cewa ya kamata a shiga siyasar Banu Umayya a dama don a zauna lafiya. Wannan abin da yake nufi kenan ko da yake shi ba haka yace ba. Kuma ya manta da cewa wanda ya assasa Political Forum din shima ‘ya’yan Malama din ‘ya’yansa ne.


KO A MAFARKI AKA CE MAKA AL-ZAKZAKY YA NARKE YA KOMA SIYASA KA KARYATA


Don an ce min cikin ‘yan siyasar ma akwai wani wanda yace ai sun ga uwar-bari ne, yanzu sun dawo siyasa, saboda ‘impression’ din da wadansu suka basu. Wato kamar mun ci wuyan tsiya ne, an kashe mana sama da mutum dubu, an rugurguza mana komai, yanzu mun ji ba dadi, mun ce to yanzu mun shiga siyasa. Nace to Allah Ya sauwake!


Ni na san cewa ko mafarki mutum ya yi, ya ji ance Al-Zakzaky yace yanzu ya narke shi dan siyasa ne. Idan ya farka zai ce mafarkin nan ya yi masa karya. Abin nan da aka sanni a kai shekara kusan 47 da suka wuce a kan haka nake, kuma Insha Allahu a kai zan bar duniya. 


Yaushe ne duk bayan wadannan kuma mutum yanzu ya rasa hankalinsa? Yanzu don Allah idan mutum yana da hankali zai yi tunanin cewa abin da aka yi mana zai sa mu yi ‘surrander’ (mu mika wuya)? Me muke bukata? Mu bukaci mene? Har abada! Ai sun mana abin da ma in ma suna neman mika wuyan ne, sun san ba za su samu ba. Me ya rage wanda za su mana.


Ballantana kuma ace mutum ya shekara 47 yana gwagwarmaya ba tsayawa, sannan kuma a sanadiyyar haka nan an kashe mutane sama da dubu, sannan an kukkule mutane, an cutar da su, ba abin da ba a yi ba, sannan kuma wai sai a ce mu yi me kuma? Me ya rage kuma? Me ya rage mana? Dan shekara 70 ya shekara sama da 40 yana Harka, sai kuma dan abin da ya rage masa mutuwa ko yau ko gobe ya ci mene a duniya? 


MASU CEWA SHA’ANIN SIYASA ZA TA WANZU KO MALAM BAI YARDA BA


Sannan kuma cikin maganganun da aka yi har da cewa wannan sha’anin siyasar nan wai haka nan zai wanzu ko da ma Malam bai yarda ba, domin haka ma Malam bai yarda da kotu ba, amma gashi ya ga amfanin kotun har yana yabo. Nace o’oh! Rashin kunyar har ya kai haka? Har ya kai haka rashin kunyar!?


Kila shine ya yi kotun ko? Domin na san a lokacin da ake ‘case’ din nan a Abuja a kotun da muka kai kara, shi lauyan gwamnati ya fadi wata magana, yace ba suna tsare da Al-Zakzaky bane, shine da kansa ya nemi kariya, -kare shi ake yi, kuma da yardarsa ake kare shi, saboda haka ba tsare shi ake yi ba. Sai shi Jojin yace, idan nace a zo da shin a tambaye shi, me za ka ce? Sai yace na janye maganar. Sai aka fashe masa da dariya kawai.


Sai yace ai shi Falana ba da izinin Al-Zakzaky ne ya zo ya shigar da karar ba. Ya zo ne kawai ya shigar da kara. Sai shi Jojin yace kana nufin lauya fitacce kamar Falana yanzu zai shigar da kara ba tare da izinin wanda yake karar ba? Yace eh haka ne. sai Jojin yace to idan nace a zo min da wanda yake karan na tambaye shi, me za ka ce? Sai yace na janye maganar. Sai aka sake fashe masa da dariya.


Ko ya ji haushi ne? (Shi lauyan Gwamnatin), sai yace to mene amfanin kotu tace a sake shi, alhali ba za a sake shi ba! Sai Jojin yace masa, kana min barazana ne idan kotun nan tace a sake shi ba za a sake shi ba? Wannan ka san abin da yake nufi? Kyamar kotu fa yake nufi. To kun san (hukuncin) kyamar kotu, nan take fa yana iya cewa a wuce da shi kurkuku yai wata shida. Sai yace ya janye, ya janye. Sai aka sake fashe masa da dariya. Wato kenan shi da kansa ya san cewa ba yadda za a yi wani ya je ya shigar da kara ba tare da izinin wanda yace a yi karar ba. 


Kuma a lokacin ma da suka yi kokarin su hana lauyan ma zuwa (wajena), suka ce min akwai wani wai Falana, akwai wani Festus Okoye, sun ce wai su lauyoyinka ne, ka san su? Nace eh na sansu. Wai sun ce su lauyoyinka ne. Nace eh lauyoyina ne. Nace akwai ma wasu karin lauyoyin ma. Na kara basu sunayen wasu, da Sadau Garba da Bello Jahun, nace duk ace su zo ina son na gansu. 


To sai wani lokaci lauyoyin da ake cema Human Right suka zo, aka basu dama suka gammu, lokacin muna nan tsare a Abuja. Sai suka ce min, gashi an kafa kwamitin bincike a Kaduna, sun je sun fadi abin da suka ce shine labarinsu, kowa ya je ya dafa, amma an ce kace kai baka yarda lauyoyinka su ganka ba ma. Nace ni!? An yi sa’a kuma duk manyan ‘yan security din suna wajen, Lawal Daura ne kawai bashi a wajen, amma na biyu da na uku a mukami baya ga shi duk suna wajen. Sai na dube su nace ni nace bani son ganin lauyana!? Sai na ga suna kokarin kar mu hada ido. Sai na kuwa kura musu ido, in na kurawa wannan ido sai ya kau da kai haka. Sai nace na san abin da ya faru, su suka je suka ce haka nan. 


To sannan ina tsaren sai gas u Falana sun zo. Yace dama abin da yake so kawai shine, ya san cewa JCI din nan sun kafa ne kawai don ta yi musu abin da suke so, saboda haka ba bukatar a kula su, mu je mu shigar da su kara, amma ba zai yiwu ya shigar da su karan ba sai na yarda. Ka yarda? Nace Eh. Ka yarda? Yace ai shi dama abin da yake so ya ji kenan.


To wani yanzu yana ‘claming’ cewa, wai ni ma ban ma yarda da kotu ba. wai amma yanzu gashi na ga amfanin kotun. Nace ko ai kaga kai, ana ma yabon Malam din ne a fake da sunansa, amma kai kace ne Malam din bashi da hankali, -bai da kan-gado. Wannan ba sukan Malam din bane? Wato har ana yin wani abin da shi Malam ma bai san amfaninsa ba, amma daga baya zai dawo ya ga amfaninsa.


MASU CEWA SHIRUN DA MALAM YA YI A KAN SIYASA IRINSA YA YI YASA SHI’A TA YADU


To kuma cikin har wala yau maganar da suka yi, akwai mai cewa shirun da Malam ya yi bai yi magana ba dangane da sha’anin siyasar nan, ai ba wani abu bane, shirun da ya yi ne ma yasa Shi’a ta yadu. Ai Malam ya yi shiru ne sai Shi’a ta yadu.


Nace wannan maganar ma da ban al’ajabi. Domin gara ma masu cewa son Manzon Allah kawai a zuciya ake yi, tunda su sun ce son Manzon Allah yana zuciya ne. To shi wannan yace in kana da wani abu a zuciyarka ko baka fada ba sai ya yadu.


Wato shi Malam din nan bai koyawa mutane bara’a ba, bai koya musu Wilaya ba, bai karantar da su Tafsirin Alkur’ani ta fassarar A’immatu Ahlulbait (AS) ba, bai koyar da su hudubobin Amirulmuminin (AS) na Nahjul Balagha ba, bai koya musu Fiqihun Imamu Jafarus Sadiq (AS) ba, bai koya musu Sira ba, bai koya musu Akhlaq ba, komai ma bai koya musu ba, ya yi gum da bakinsa ne.


(Kai kace) bai kuma raya Munasabobi ba, bai raya Munasabobin Mauludai ba; Miladin Annabi, da Makon Hadin-Kai, da Miladin Amirulmuminin (AS) da na Sayyida Zahra (SA) da na Hasan da Husaini (AS) da sauran A’imma (AS), da kuma Maqtal dinsu (Shahadodinsu), bai yi magana dangane da Shahadar Annabi (S) ba, bai yi magana kan Shahadar Amirulmuminin da Sayyida Zahra (SA) ba,  bai yi magana kan Shahadar Imam Hasan ba, bai yi Ashura da Arba’in ba, duk Munasabobin nan duk bai raya su ba, bai yi Milad din Sahibul Asr Waz Zaman (As) ba, bai cewa kowa komai ba, ya yi gum da bakinsa ne gum sai duk Shi’a ta yadu.


Me yasa ta yadu? Ya yi gum da bakinsa. Wai Shi’a ta yadu ne saboda Malam ya yi shiru. Wannan balidanci har ina!? Ko dabba aka ce ta yi magana, za ta yi maganar da ya fi wannan hikima. Ashe idan idon mutum ya rufe sai basirarsa ta dode haka nan? Yanzu tunda akwai wani abin da yake so ya tabbatar, da abin da baya so, sai kawai basira ta dode ya rika sakin maganganu haka?


Za mu cigaba.

—Cibiyar Wallafa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post