@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Namiji Nagari a yau ba wai ana samun sa bane ba ta hanyar zahirinsa, sai kin yawaita tsayuwar Dare da yawaita Addu'a sosai, kiyi Qoqari ki karanci Namijin da kike tare da shi, baki sanin Halin mutum sai kin zauna da shi, Namiji yana da Hankali, Dabara, Hikima, wayo, ta yanda sanin shi ma sai wanda nace miki ki roqa shi zai sanya miki mafita ya zaɓa miki, shi yasa nace miki ADDU'A, sannan ki kalli abu 5.
(1) Qarfin tausayinsa, musamman qarfin kulawar shi ga iyayensa da yanda yake mutunta su da yanda yake mu'amala da ƴan uwansa mata kar kiyi mamaki ina da dalili.
(2) yanda ya ɗauki Rayuwa da Duniya da mu'malarsa da Halittun Allah, ina me miki wasiyci ki zaɓi me Son Allah da yi don Allah.
(3) Gaskiyar sa, ki Auna ta sosai, Qarya ana mantata, amma banda gaskiya.
(4) cika Alqawarinsa, da Amanarsa.
(5) Qarfin kame kansa daga zinace-zinace da ya yawaita a zamanin nan, wanda ya neme ki da zina ba kanki ya fara ba, kuma ba kanki zai gama ba (Ba kowanne Namiji ne yake da kame kai ba duk Ilimin Addininsa, kyauta ne daga Allah, sai kiga wanda yake error a Fatiha zina bata burge sa ko saɓon Allah saboda yana Son Allah da jin tsoronsa gwargwado). Ina roqon Allah ya iya miki....