Makarantar Elsa, makaranta ce wacce ta ke koyar da Harshen Turanci a garin Zariyar Jihar Kaduna. Ta na gudanar da karatuttukan nata ne a Makarantar Sakandare na mallakar Gwamnatin Jihar Kaduna da ke kofar Doka Zariya.
Makarantar ta yi zara kwarai ta yadda ta ke da dubban dalibai da ga wurare mabanbanta, Kuma kabilu mabanbanta. Wannan dalili ne ya sa Hukumar Makarantar ta yi yunkurin gudanar da bikin Al'adu don ilimantar da Daliban Makaranta.
Ta Kuma Sami gudanar da bikin Al'adun ne a ranar Asabar 17 ga watan Disamba, a filin Makarantar Sakandare na Kofar Doka.
Daliban Makarantar sun gudanar da bikin Al'adun ta hanyar shiga irin ta: Hausa, Yoruba, Igbo, Kanuri da Nupe, don koyar da Al'adun wadannan kabilu.
Taron ya Sami halartar manyan baki, malaman makarantu, masu sarauta, iyayen Yara da sauran Al'umma da ga wurare daban-daban.
- Salisu Jibril Khidir