@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Bayyana tsiraici alamu ne na fushin Allah, shi yasa lokacin da Allah ya yi fushi da Annabi Adam da Hauwa sai ya bayyana musu tsiraicinsu. (فَأَكَلَا مِنْهَا فَبَدَتْ لَهُمَا سَوْآتُهُمَا)
Wata baiwar Allah ta ke cewa: Duk lokacin da naga mace ta sanya tufafin banza ko kuma tana yawo tsirara sai in tuno iyayenta ya zasu yi da faɗinsa maɗaukakin sarki: (وَقِفُوهُمْ ۖ إِنَّهُم مَّسْـُٔولُونَ), Ma'ana: "Ku tsayar dasu, haƙiƙa su ababen tambaya ne (dangane da amanar da aka basu)."
Tace: sai in ƙara jin kunya domin tsoron kar Allah ya tambayi Mahaifina da Mahaifiyata.
Mafiya yawan ababan da Allah ya haramta a duniya (irinsu giya) ya halatta su a Aljannah amma ban da bayyana tsiraici domin Allah (swt) Cewa ya yi: (إِنَّ لَكَ أَلَّا تَجُوعَ فِيهَا وَلَا تَعْرَىٰ)
Ma'ana: "Haƙiƙa (Ya Ãdam) a cikin aljannah ba zaka ji yunwa ba sa'annan kuma ba zaka bayyana tsiraici ba."
YANA DA KYAU, A GIRMAMA HIJABI, DA MASU SANYA HIJABI
Haqiqah Hijab lullubi ne, mai Qawatah diya Mace, ta hanyar rufe surar jikanta, ba tare da bayyana tsiraici, koh bayyana shi ga wanda bai chanchanta ba.
Da hakane ALLAH (SWT), Yayi umurni ta bakin Manzon Allah (SAWW), cewa: Matayen Musulmi, su lullube jikinsu da mayafi wadatacce, domin kubuta daga zargi, da kare mutunci".
Amma ayau, Hijab ya zama abinda izgili da wulakantawa tsakanin Musulmi. Wasu sun dauke shi tamkar Qauyanci da wawanci, alhali sune wawaye Qauyawa ga karantarwar Addinin Musulunci.
Don haka; Mata ku killace jikinku domin Mazajenku, kuma kada ku tallata jikinku ga wawayen da basu san darajarku ba.
IYAYE; Ku taimaki ƴaƴanku wajen yi musu tarbiyya ta gari domin wallahi sai Allah ya tambayeku dangane da amanar da aka baku ta ƴaƴanku.
Haqqin da yake kanka ka fara saukeshi Kafin ka Nemi Wanda za a baka a matsayinka na Uba. Allah Yasa Mudace....
Tags:
Tunatarwa