Bayan buɗe wutan, tawagar ta Buratai ta wuce, sai waɗancan kuratan sojojin da aka kawo da farko suka cigaba da kewaye Husainiyyah, aka riƙa ƙaro musu ƙarfi.

 

Gidan Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) da Gwamnatin Buhari Ta Ƙona

Kashi Na 2:


Daga Littafin KISAN-KIYASHIN ZARIA DA ABUBUWAN DA SUKA BIYO BAYA.


WALLAFAR: Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)


Babi na farko:


KISAN-KIYASHIN ZARIYA


A ranar Alhamis, 28 ga Safar 1437H, daidai da 10/12/2015, bayan kammala zaman juyayin ranar wafatin Manzon Allah (S), Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayar da sanarwar taron saka tutar Maulud, wanda ya ce za a gudanar a yammacin ranar Asabar 1 ga watan Rabi’ul Auwal, 1437 (12/2/2015).


A shekarun da suke gabanin nan, sojoji sun saba gabatar da bikin yaye sabbin kuratan sojojin a Zariya a duk ƙarshen shekarar Miladiyya a ranar Juma’a da safe. Sai dai a wannan shekarar, ba zato ba tsammani sai suka maishe da bikin nasu ya koma Asabar 12 ga Disambar 2015, kuma da yammaci, maimako Juma’a da safe kamar yadda suka saba gabatarwa a tsawon shekaru. Wannan ya ba su damar ya zama rana da lokacin bikin nasu ya yi daidai da rana da lokacin taron sauya tutar Mauludi da Harkar Musulunci ta ayyana za ta gabatar a Husainiyyah Baqiyyatullah a wannan ranar.


Harkar Musulunci ba ta yi tunanin ɗage taronta a wannan ranar ba, ganin cewa wuraren da za a gudanar da taruka biyun ba kusa suke da juna ba, don haka babu wani abu da zai haɗa masu gudanar da taron sauya tutar Maulud da masu yayen sabbin kuratan soji a waje guda, ko hanya ba za ta haɗa su ba. 


Sai dai wani abu da ba a yi zato ko tsammani ba, da misalin ƙarfe 12:15 na ranar Asabar ɗin, wata babbar motar Sojoji ta zo ta sauke wasu dandazon kuratan sojoji ɗauke da makamai tare da akwatu harsashi, a daidai gaban Husainiyyah Baqiyyatullah. Wannan abin ya yi matuƙar ba ‘yan uwan da ke wajen mamaki har suka yi ƙoƙarin tuntuɓar sojojin dalilin da ya sa aka kawo su gaban Husainiyyah a daidai wannan lokacin, amma sai sojojin kawai suka fara harbi a sama a matsayin amsar wannan tambayar. Daga baya ma sai suka fara kewaye wajen suna harbi. Sai ‘yan uwa suka ba kansu kariya ta hanyar matsar da su daga gaban Husainiyyar da kabbarori da neman taimakon Ubangiji.


Bayan kamar awa guda da faruwar wannan lamari ne, misalin ƙarfe ɗaya na rana, sai ga tawagar Janaral Buratai ta biyo ta wajen Husainiyyar da sunan za ta wuce. Kai ka ce tawagar ta shugaban rundunar sojojin Nijeriya ba ta san da hatsaniyar da ke faruwa a wannan wajen ‘yan mintoci da suka gabata ba, wanda a ƙa’idar tsaro, abin zai tilasta musu haƙura da bin hanyar da samun wata da babu kowane irin barazana a tattare da ita in har ba wani nufi suke da shi ba.


Zuwansu, tare da masu ɗaukar hotuna cikin kakin sojoji, sai suka shirya wani abu kamar wasan kwaikwayo. Suka yi fuska, tare da nuna rashin sanin faruwar wani abu da wasu kuratan sojoji suka gabatar a wajen kafin zuwansu. A yayin da wasu ‘yan uwa suka tunkare su don su ji ko da me suka sake dawowa wajen za su yi? Sai wasu jami’an tsaro a cikin rigar ‘yan uwa Musulmi (kamar yadda shugaban DSS na Zariya ya bayyana a gaban JCI, cewa akwai mutanen su a cikin ‘yan uwa a wannan ranar a Husainiyyar) suka riƙa ihu, tare da ɗaɗɗaga sanduna ga sojojin. Nan take sojojin suka buɗe wuta kan mai uwa-da-wabi.


Bayan buɗe wutan, tawagar ta Buratai ta wuce, sai waɗancan kuratan sojojin da aka kawo da farko suka cigaba da kewaye Husainiyyah, aka riƙa ƙaro musu ƙarfi. A yayin da suka bi suka kwashe gawarwakin waɗanda suka harba suka saka su a mota suka tafi da su. A shirin rana na BBC a wannan ranar, sai ga hirar kakakin rundunar soja na wancan lokacin Sani Usman Kukasheka, inda yake bayyana cewa, an yi kwanton-vauna ga shugaban rundunar sojoji ne, har ma ya tsallake rijiya da baya. Zargin da nan take shugaban ɓangaren yaɗa labarai na Harkar Musulunci a wancan lokacin, Malam Ibrahim Usman ya musanta.


Kamar yadda ta bayyana a cikin cikakken bidiyon wannan harin da Harka Musulunci ta sake daga baya, wanda ke da tsawon awanni, Sojoji sun ci gaba da kewaye Husainiyyah, tare da harbin duk wanda suka samu a kewayenta, har zuwa ƙarfe 5 na yamma, lokacin da gwamnan Kaduna, Nasiru Ahmad El-rufa’i ya zo wajen Husainiyyar. Bayan magana da ya yi da jagororin sojin, sai ya yi gaba. Wucewarsa ke da wuya sojoji suka ƙara tsananta harbe-harbe a Husainiyyar, tare da yunƙurin shiga cikinta ta kowane hali don su rusa ta.


Ana cikin wannan halin har dare ya shiga, da misalin karfe 10:30 na dare, sai ga wasu sojojin sun kawo hari gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da ke unguwar Gyallesu, kilo-mita kusan biyar daga Husainiyyah Baƙiyyatullah. Zuwan su ke da wuya suka yi burki a daidai ginin Banaden, kan kwanar layin da zai kai ka gidan Shaikh Zakzaky, suka jefa wani abin fashewa a shagon wani mai shayi, bayan wuta ta kama sai suka riqa amfani da hasken wutan da ke ci wajen saitowa da harbe duk wanda suka gani a kan wannan layin.


Sojoji sun kwana suna harbi a wannan ranar Asabar 12 ga Disambar 2015 ɗin, har zuwa wayewar garin Lahadi, inda suka yi nasarar kashe duk wani mutum da ke gidan Shaikh Zakzaky da suka haɗa maza, mata da ƙananan yara, tare da jikkata saura. Suka kuma watsa fetur akan gawarwakin ‘yan uwa da kuma wasu ‘yan uwa masu rauni da ake ajiye su a wani gida kusa da gidan Shaikh ɗin, suka banka musu wuta suka qone ƙurmus. Sannan suka tattaro gawarwakin waɗanda suka kashe akan layi, suka tara su waje guda, suka ba mutanen unguwa damar su caje aljihunsu su sace abin da suke so daga jikin gawarwakin.


Za mu cigaba.

📰 Journalist

Dan Fudiyya

4 Dec 2022


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM


@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/


@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/


DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN


@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post