@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Zinar ido (wato kallon abinda Allah ya haramta) da kuma zinar jiki da jiki, dukkaninsu laifuka ne masu girma. Domin kuwa Allah ya haramtasu acikin Alqur'ani da kuma hadisai daga Manzo Allah ﷺ .
Zinar ido tana daga manyan hanyoyin da Shaidan yake bi domin jan mutane zuwa ga aikata zinar jiki da jiki. Shi yasa ma Allah yace wa Annabinsa ﷺ "Ka gaya wa muminai maza su runtse idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu, wannan shi yafi tsarkakewa gareku. Hakika Allah masani ne game da abinda suke aikatawa".
Imam Ibnu Katheer yace : "Wannan umurni ne daga Allah (SWT) zuwa ga bayinsa Muminai cewa su runtse idanuwansu daga kallon duk abinda ya haramta musu. Kada su kalli komai sai abinda ya halatta musu kallonsa".
Manzon Allah ﷺ ya fa'da acikin wani hadisi cewa "Kallo, wani kibiya ne mai dafi (poison) daga kibiyoyin iblees. Duk wanda ya barshi (wato ya bar kallon) domin tsorona, zan chanza masa da wani imani, zai ji dandanonsa acikin zuciyarsa".
(Tabaraniy ne ya ruwaitoshi).
2. Ita kuwa zinar jiki da jiki, ai Manzon Allah ﷺ yace "Bayan yin shirka da Allah, babu wani zunubi mafi girma kamar maniyyin da wani mutum ya sanya acikin mahaifar da bata halatta gareshi ba". Kuma yace "Mazinaci ba zaiyi zina alhali yana mumini ba". (Wato sai bayan an cire masa imani).
Zinar ido babu haddi akanta. Amma zinar jiki da jiki, in dai shaidu suka tabbata akan masu laifin, ko aka samu Iqirari tabbatacce daga masu laifin, ana yi musu haddin bulala dari (100) idan basu ta'ba aure ba. Idan kuma sun ta'ba yin aure hukuncin rajamu ake musu (wato jefesu da duwatsu har sai sun mutu).
Kuma Manzon Allah ﷺ ya bada labarin dake nuna cewar koda acikin wuta, mazinata wajen azabtar dasu ya bambanta, yafi muni fiye da na sauran 'yan wuta.
(Allah Ya kiyayemu da aikata zina, kuma ya kiyayemu daga shiga wuta. Ilaheey Ameen).
Tags:
Tunatarwa