Rubutawa: Ammar Muhammad Rajab
"" Ranar 12 ga watan 12 na shekarar 2015, da misalin karfe 1:30 na rana, koma na ce karfe 12 da mintoci, aka fara shiga halin firgici, domin rana ce da ba zata taba gushewa ba a zukatan al’umma musamman mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (h).
A wannan rana ne a lokacin da Harkar Musulunci a Nijeriya take shirye-shiryen dora Tuta a Kubbar Husainiyyah Bakiyyatulllah, domin murnar shiga watan Rabi’ul Awwal, watan daaka haifi fiyayyen halitta, Manzon Allah (saww), su ko makiya wannan Manzo (SAWW) a lokacin suka shirya wata tuggu da makirci na ganin an kawo karshen Harkar Musulunci a Nijeriya wanda Shaikh Ibraheem Zakzaky yake yiwa jagoranci, wanda suka yi amfani da shugaban Hafsan Sojojin Nijeriya, T.Y Burutai wajen fara aiwatar da shirin na su wanda kasashen Amurka, Isra’ila da Saudiyyah suka ba da kwangila.
Al’amarin ya fara ne kamar a mafarki, a lokacin da Sojojin Nijeriya cike mota kirar TATA suka taho daga Barikin Soja na Depot dake titin Rwarf road Sabon garin Zariya, da rana tsaka suka sauka a bakin Husainiyyah Bakiyyatulllah tare da sauke akwatunan harsasai, jim kadan kuma sai ga tawagar T.Y Burutai ta iso inda suka zo da yaudarar cewa a basu hanya su wuce, kuma nan take suka hau kisan ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky mabiya Harkar Musulunci.
A lokacin wannan ta’addanci da Sojojin gwamnatin Nijeriya suka yi bisa hujjar cewa an tare wa shugabansu Tukur Yusuf Burutai hanya, dalili mara tushe bisa dokar ilimi, hankali da hujja. Sojojin sun kashe dimbin almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a nan Zariya.
Da misalin karfe 10:30 na daren ranar Asabar 12 ga watan 12 na 2015, Sojoji suka je Gyallesu inda Shaikh Ibraheem Zakzaky yake da zama da iyalansa, daga zuwansu suka fara harbin kan mai uwa da wabi, ba gaira ba dalili akan duk wanda suka samu akan hanyar zuwa gidan Shaikh Zakzaky.
Wannan dalilin yasa mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya suka baiwa jagoransu kariya da jikkunansu, wanda Sojojin gwamnatin Nijeriya suka kashe dubban mabiya Harkar Musuluncin, tare da sace da dama zuwa wasu muhalllan da ba a sani ba. Da kuma raunata da daman gaske.
Tun a cikin wannan dare na ranar Asabar din 12 ga watan Disamba, ganin yadda Sojojin suke kisan kiyashi na ba gaira ba sabat, al’umma da dama musamman a Nijeriya suka fito muzaharori a wannan dare domin nuna rashin amincewarsu da wannan aika-aika da Sojoji suke aikatawa.
Garuruwan da aka fito sun hada da: Kano, Kaduna, Katsina, Saminaka da dai sauran su.
Daga cikin ta’addancin da Sojojin gwamnatin Nijeriyasuka aikata a gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky sun hada da; kona mutane da ransu, karasa kashe duk wani mai rauni da suka gani, sannan suka kashe mata da kananan Yara da kuma tsofaffi. Har wala yau duk a wannan muhallin sun kashe ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky guda Uku wanda ya hada da; Hammad, Ali da Humaid. Sannan sun kashe dan Yayan Shaikh Zakzaky wato Shamsudeen Abdulkadir. Duk a cikin kisan rashin imani da Sojojin suka aikata, sun kashe Yayar Shaikh Ibraheem Zakzaky wato Gwaggo Fatima Ya’qoub. Sojojin sun yi amfani da dukkan nau’in muggan makamai wajen aikata wannan kisan, a inda karar harbe-harben na su yake fitar da nau’ukan kara daban-daban.
Duk da halin matsanancin sanyi da ake yi a irin wannan lokaci musamman a ranar wannan Lahadi ta 13 ga watan Disamba, amma ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky sun tsayakyam suka sadaukar da rayuwarsu domin ceton jagoransu. Bayan Sojojin sun kashe duk wani abu mai motsi a kofar gidan Shaikh Zakzaky da ranar wannan rana, sannan suka samu suka cimma gidan a inda suka yi kisan kare dangi a cikin gidan ta hanyar harbi da cinnawa gidan wuta.
Har wala yau sun kama da dama zuwa Barikin na su na Soja a inda suka yi ta azabtar da su ba tare da samun kulawa ba ko ba su abin da za su ci ba.
Washegarin ranar Litinin ne 14 ga watan Disamba, ta sanadin wani mutum da suka dasa a gidan ya kirawo Sojojin da safe (kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar), ya nuna wani daki ya tabbatar musu cewa; akwai mutane a wurin, a inda suka shigo suka yi ruwan wutan harsasai a wannan dakin wanda ta kai ga raunata Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Zakzaky akalla da harsasai 6 (sahihin zance ba wanda ya san ko adadin harsasai nawa jikin Shaikh Zakzaky) a wurare da daban-daban, wanda ya hada idonsa, hannuwasa da kafafunsa, sannan suka raunata matarsa, Malama Zeenatuddeen Ibraheem, tare da kashe ‘ya’yansa guda Uku akan idonsa; Hammad, Ali Haidar da Humaid, wandadaga karshe suka tafi da su baki dayansu da wadansu wadanda suka rayu tare da su. Daga cikinsu akwai ‘yar Malam Zakzaky wato Suhaila Ibraheem Zakzaky, Zainab Hameed Danlami da Sajida Aminu Yabo da sauran su.
#ZARIA_MASSACRE. .
#Freedom_For_Zakzaky
#No_To_Injustice.
#We_Demand_justice.