Babu Abinda Zai Rage Ni Ko Ya Kare Ni Don Sahabi Ya Zama Dan Alhannah Ko Dan Kuma Dan Wuta..!!!


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


Page 2


Babbar ayar da ta zama dutsen fashin tama Akan adalcin duk kan sahabbai ita ce wacce take cikin suratul FATHI aya ta goma sha takwas, wadanda suka Yi bai'a a qarqashin bishiya,!  lokacin yarjejeniyar hudaibiyya,  wacce aka ce Manzon Allah sallallahu alaihi wa aleh ya nemi sahabbai suyi masa ita Akan fansar kashe saiyidina Usman da ake zargin Quraishawa da yi bayan ya tura shi ya zama jakadan sa Akan yarjejeniyar zasu bar shi Ya shiga Garin makka Don gudanar da aiyukan ibada

 Duk da an murda tarihi anan Ana yawan ambaton Quraishawa saboda Manzon Allah sallallahu alaihi wa aleh ya fi to daga cikin qabilar ne kuma sune suka fara yin adawa da shi ya karya lagon su a tsakanin badar da uhud , sannan da son tsakake Qabilar umaiyawa! Amma makka a wancan lokacin hudaibiyya, tana hannun umaiyawa ne qarqashin jagoranta wato Abu sufyan, lokacin da annabi ya wakilta saiyidina umar yaje Yayi Magana da su, sai ya gabatar da uzuri cewa akwai tsohuwar gaba a tsakanin sa da su in yaje zasu kashe shi, sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa aleh Yayi wa Dan qabilar su Abu sufyan din, wato Uthman Dan affan shi yaje,  


Mu yanke duk wannan dogon tarihin mu je ga albishir din da ayar tayi musu a wannan bai'a da su Ka yiwa Manzon Allah sallallahu alaihi wa aleh,, to sahabban da suka je hudaibiyya gaba daya su 1400 ne kawai,  kuma iya su kadai Allah ya ambata tun da ya fadi cewa wadanda suka yi Maka wannan bai'a ta qarqashin bishiya,   duk wani wanda ya zo a wajen wadannan adadin?  To Allah ya yarda da shine kawai Idan ya aikata Abinda Allah Yayi umarni a aikata cikin suratul Baiyina aya ta 7, sannan yace kuma ya yarda da wadannan mutanen a aya ta takwas dake cikin wannan surar, cikin ta kuwa har ni da kai ba sahabban kawai ba zamu iya shiga cikin yardaddun Allah matuqar an yi irin wancan aikin, anan Babu fifiko, 


Lokacin fathu makka, akwai sahabban da aka je yaqin da su,  su goma sha biyu  musulmai ne tun farkon Hijira kuma sahabbai na kwarai, Amma bayan yaqin, kuma sune Abu Amir al rehab ya jagoranta suka gina masjidul Dhirar!  Da Allah Yayi musu fatafata a cikin suratul tauba aya ta 107,sannan Allah ya hana Manzon Allah sallallahu alaihi wa aleh yaje ya Bude musu masallacin Don ayi sallah bayan dawowar sa daga filin Tabuk!  A Qarshe Manzon Allah ya sa aka rushe ko kuma Qone masallacin!  Duk duniya ta musulunci an yarda su din munafukai ne har Ana cewa na can Qololuwa ,  Amma me ya sa aka dinga 6oye Sunan su,  ake baiyana Sunan shugaban su wanda shi bai ta6a musulunta ba? 


Maganar cewa duk wanda Yayi imani da Manzon Allah sannan ya zauna tare da shi ya kuma temake shi shine SAHABI!  To ga wasu muna lissafowa tun kafin Yayi wafati suna warware alqawarin su,  me kake zato kuma zasu yi bayan basa ganin idanun sa?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post