Ba Muna Kyama, Ko Haramta Auren Ba'ama Bane, A'a Akwai Abunda Muke son Burazu mu Su Fahimta_ Nusaiba Ahmad Bauchi



Lallai duk wani wanda ya tsira dole yaso iyalan sa ma su tsira Babu wanda zai so yana cikin haske ya koma Duhu. ..... Amma ta ya ya za'ayi su tsira? shi ne tambayar.. 

Duk da munsan shi tsira da shiriya yana daga wajen Allah (T). 


Sannan kuma shi Allah da kansa ya ce "Ku tunatar domin ita tunatar wa tana amfanar muminai ne"


Shin za su tsira ne ta hanyar nuna rashin darajta 'yan uwan taka da rashin soyayyar gaskiya a tsakanin Al'umma ne? Shin ma me ne ne Addinin Musulunci kan ta gaba ɗaya? Na ji wani malami ya ce Imam Ali (A.S) ya ce Addinin Musulunci shi ne Soyayyar juna tsakani da Allah.


_Tambaya Shin Me yasa a Ka ce 'yan uwan taka na addini ya fi na jini? 


_Tambaya Shin wani hadafi ne ya haɗamu? 


Shin zamu ciga ba da Ce_ce kuce da ƙaƙaba Laifuka wa junan mu ne ko kuma? 


A tunanin ku idan ba mu gyara kawukan namu ba, maganar da jagora ya faɗa akan muzama jakadu a duk inda muke. da irin wannan rashin soyayyar zamu zama jakadun.?


Na'am; Fatan mu shi ne wasu su samu shiriya daga gare mu. to a irin wannan ɗabi'u namu ne idan wasu suka shigo cikin mu zamu tafiyar da su? kodai in sun shigo cikin mu zamu watsar da tarbiyyar da Jagora ya mana na soyayyar juna da tau saya wa juna ne mu ɗauki nasu wanda suka zo da shi?.


Kada ku mance da duk wani wanda yaga wannan hanyar ita ce mafita a gare shi har yazo cikin mu, to fa abun da ya ɗauru akan mu shi ne muyi abun da jagora ya koyar damu ta yadda zai ƙara samun yaƙini, bawai muyi abun da zai kora shi ba.


_Mu gyara kawukan mu sannan kuma mu ƙaunaci junan mu tsakani da Allah, mu kuma alamtu da Addini a aikace ta yadda idan wasu suka dube mu zasu ɗauki darasi ta soyayyar juna tsakani da Allah tare da yinta bisa yadda Addi ni ya shimfiɗa.


Mu Rahma ne ga al'umma kuma muna da hadafin da yasa muka ce addini zamu yi kuma dole duk abin da addini ya shar'anta mu bi ta in har ba yaudarar kan mu zamu yi ba.


Cikin wannan tafiyar akwai tausasawa ga al'umma, to dole sai munji tausayin su sannan zasu iya fahimtar me muke nufi.  


To idan har da gaske tausasawar muke musu wani sa'ayi mukeyi wajen isar musu da saƙon su jagora (H). Shin mu karan kanmu abin da jagoran yake faɗa shi muke yi? 


Muji tsoron Allah wallahi muji tsoron Allah. bazamu taɓa yi wa Allah wayo ba na cewa ai naje wajen Ba'amiya ko Ba'ame ne domin Aurenta ta ko Auransa ta hanyar ne ma zata /zai  iya fahimta tinda tana /yana sona. to Dan  Allah baku tashi fahimtar da su ta hanyoyi da dama ba sai dan kana sonta  ko kina sonsa ne zaka/zaki  fahimtar da ita/shi?


Ya kama ta mu fahimci cewa. 


Ba sai kina san Ba'ame ko kana san Ba'amiya zaka fahimtar da su wannan tafiyar ba. wajibine a gare ka ka fahimtar da dukkan Al'umma ne ba iya wanda kuke da burin rayuwa ba. Na'am bazaku iya fahimtar da kowa ba Amma idan ana sa'ayi duk rintsi wasu zasu fahimta. kuma ita wannan fahimtarwar Akwai hanyoyi da dama da zakabi dan fahimtar da mutum a aikace ba ma sai da baki ba.


Abun da muke ƙara cewa shi ne lallai sai mun gyara kanmu tukunna duk wanda yazo cikin mu zai iya fahimtar abin da muke cewa da abin da muke aikatawa. 


wannan tinanina ne... 

zan kuma cigaba insha Allah.

✏️Real Nusaeberty.


Allah ya tsare mu ya tsare mana imanin mu. ya tsare mu da biye wa son zukatarmu. ya haɗa kawukan 'yan uwa, ya bamu ikon gyara kawukan mu ya kuma tabbatar da mu duk tsanani duk wuya.🤲

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post