Ba mu gamsu da hukuncin da aka yanke wa Sheikh Abduljabar ba, in ji almajiransa

 


Almajiran Sheikh Abduljabbar sun ce akwai abubuwan da ba su gamsu da su a cikin hukuncin kotun da yanke wa Malaminsu.


Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da mai shari’a na babbar kotun musulunci ya same da laifin aibata Fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).


Kamar yadda wa'azinsa da shari'ar ke cike da cece-kuce haka ma hukuncin kisan da aka yanke masa ta hanyar rataya, shi ma a yanzu yana tattare da wannan ka-ce-na-ce din.


Yayin da wasu mutane da dama suke ganin hukuncin ya dace da tuhume-tuhumen aikata sabo a kan fiyayyen halitta da aka samu Sheikh Abduljjabar da laifi, wasu kuma musamman wasu dalibansa suna cewa ba a yi la'akari da hujjojin da malamin nasu ya gabatar a gaban kotun ba a wajen yanke hukuncin.


Sai dai kuma daliban nasa sun shaidawa BBC cewa su masu biyayya ne. Amma a cewarsu shari'ar tana cike da ayoyin tambaya.


Wannan hukunci na yau dai, shi ne kusan babban labarin da ya karaɗe ba kawai jihar Kano ba, har ma da sassan musamman arewacin Najeriya.


Akasari dai hukunci irin wannan ya kan zamo babban kalubale musamman ga mahukunta wajen zartar da shi.


Babbar kotun Shari'ar dai ta ce yana da kwana talatin ya daukaka kara.


Yanzu dama ta rage ga Sheikh Abduljabbar, duk da yake har lokacin da ake yanke masa hukunci yana cewa bai aikata laifi ba.


Sai dai batun mika wuya ga hukuncin yanzu za a zuba ido a gani ko zai yi amfani da wannan damar ko akasin haka.

Hoton farko Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Hoto na biyu Alkali Ibrahim Sarki Yola

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post