Inji sheikh turi
Mu a gurin mu baza a taba samun wata mafita a siyasa mafitar shine a koma a bi tafarkin Allah(S)Mu a gurin addini shine yake gyara mana duniyar mu da lahira. Misali kamar kasar mu Nigeria irin yawan matsalolin da muke fama dashi bamu da wata mafita face a koma hanyan Allah(S)Mu a gurin mu addini yana gyara tsakanin mutane ne, kuma yana gyara tsakanin mutum da Allah(S).
Shi yasa muke kara kira cewa idan mutum kasan nan suna bukatar mafita,to Allah(S)ya tayar da Sayyid Zakzaky(H)Wanda ya kasance yanzu su Sayyid(h)suna kira ga tafarkin tsira.Kuma wannan al'amari na Mallam ya tara kowani bangare a wannan kasa tamu. Shi yasa idan muna tarukan ma mukan gayyato ko musulmi da wanda ma ba musulmi ba suyi musharaka da mu.
In bamu manta ba akwai wani taro da mu taba yi bayan sallah a Hussainiyya Bakiyatullah a watan zulhijja ya zamana cewa akwai shuwagabannin Christian da suka zo daga Kaduna wasu kuma daga Jos.Daya daga cikin su sai yake cewa shi abin da yake so shine a bude ma Christian wani reshe karkashin Islamic Movement. Sai su Sayyid(H)ya basu amsa da cewa "Eh a wannan harka din akwai janibobi daban-daban, akwai bangaren dalibai(Academic Forum) sannan kuma akwai bangare na tayar da 'yan jami'a(Resource Forum)saboda haka an bude Christian Forum.Shi yasa zaku ga wasu kiristocin dasu muke mu'amala. Kaman Fasto Yohanna Buru dashi bana muka yi tattaki(Shekarun baya)Saboda shi yace yana tare da Imam Hussain(As)tunda yana fada da zalunci.Kuma yin musharaka da kiristoci wannan ba bakon abu bane a musulunci.
Bamu yarda cewa kungiyoyin siyasa sune zasu canja kasar nan ba. Amma idan mutum ya mai da kansa wawa toh wannan kuma ya rage nashi,amma siyasa da 'yan siyasa baza su warware matsalar sa ba.Su wadannan mutanen da suka zalunce ka a baya sune suke dawowa su canza jam'iya, suce sun bude jam'iya da zata kawo sauyi.Da yake mutane mahaukata ne sai suyi ta murna an samu sabuwar jam'iya.