Cewar wani dalibinsa.
Babu shakka siyasa ta taka Muhimmiyar rawa cikin mas'alar Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara (H) , sai dai cewa al'amarin yafi haka girma da faɗi , a taƙaice dai za mu iya cewa abubuwa shida suka haɗarma Sheik Abduljabbar har aka kai ga halin da ake ciki :
1 . Ƴan Siyasa da miyagun Mahukunta da suke da matsala ta musamman da shi .
2. Ƙiyayya da hamayyar gado da wasu ƴan Ɗariƙa suke yiwa mahaifinsa tun shekaru masu yawa , shine ƴaƴansu suka gada daga gares u suka ɗorata akan Malam Abduljabbar a bayan mahaifinsa shima .
3 . Hassadar ɗan Uwa , da Hassadar wasu malaman dai da sun haɗa wasu Malaman Ɗariƙa da Wahhabiyawa Salafawa .
4 . Fafatawa da ya kwashe Shekaru yanayi tsakaninsa da Wahabiyawa Salafawa da Saudiyya ke dafawa dan ganin kawo karshen Sufanci da Shi'anci a Najeriya , da suka ga sun kasa ganin bayansa sai suka haɗu da waɗancen ƴan Ɗariƙa ko haƙar su ta cimma ruwa .
5. Wauta da Jahilcin mabiya Malaman Maja dama wasu mutanen gari da basu san daga inda aka fara ba .
6 . Amfani da wasu kalmominsa da suka shafe tsawon Shekaru suna jira yayi su dan su riƙe su a matsayin tarko da wasiɗar isa ga burinsu akansa ta hanyar amfani da Gwananti, shi yasa Mas'alar ta fi bayyana da rigar Siyasa amma ba iya siyasar bace .
A taƙaice dai akwai lauje cikin naɗi a mas'alar Sheik Abduljabbar (H) , babu mai iya fahimtar haka sai mai hankalin yin adalci .
#Ya Jabbaru kai nasara ga Abduljabbari 🤲
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey