[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
-An Ruwaito Hadisi Daga Ummul A'imma Sayyada Fatima (AS), lta Kuma ta ji Daga Mahaifinta Manzon Allah (S), Sayyada Fatima Tace: "A Lokacin da Manzon Allah Ya Dawo Daga Tafiyar Isra’i da Kuma Mi’iraji, Sai Yace Min Naga Wasu Mata A Cikin Wuta Ana Azabtar Dasu A Kan Wasu Laifuffuka da Suka Aikata A Rayuwarsu ta Duniya.
-Manzon Allah Yace: "Akwai Waɗanda Aka Ɗaure su da Gashin Kansu Ana yi Musu Azaba, Wasu Kuma An Ɗaure su da Harshensu, Wasu Kuma da Nononsu, Wasu Kuma An Daure Ƙafafuwansu da Hannayensu, Wasu Kuma Suna Cin Naman Jikinsu.
-Akwai Wasu Mata Kuma An Daure Su Sannan ga Kunamai da Macizai Suna ta Saran Jikinsu. Akwai Wasu Masu Fuskar Alade da Jikin Jaki, Akwai Wasu Mata Masu Surar Kare.
-Sai Sayyida Fatima (AS) Ta Tambayi Manzon Allah (S) Dangane da Ayyukan da Suke Aikatawa,
-Sai Manzon Allah (S) Yace, “Wadda Aka Ɗaure ta da Gashinta ta Kasance Bata Rufe Gashinta ga Mazaje.
-Wadda Aka Ɗaure ta da Harshenta ta Kasance Tana Cutar da Mijinta Da Munanan Kalamai.
-Wadda aka Ɗaure ta da Nononta ta Kasance Tana Hana Kanta ga Mijinta.
-Wadda Aka Ɗaure da Kafafuwanta ta Kasance Tana Fita Daga Gidanta Ba Tare da Izinin Mijinta Ba.
-Wanda Kuma Take Cin Naman Jikinta ta Kasance Tana Qawatar da Jikinta Saboda Mutane.
-Wadda Kuma Aka Ɗaure Hannayenta Tare da Ƙafafuwanta aka Kuma Haɗa ta da Macizai da Kuma Kunami ta Kasance Bata Wankan Haila da Wankan Janaba Tana Kuma Wasa da Sallah.
-Wadda Kuma ta Kasance Kanta Kan Alade, Jikinta Kuma Jikin Jaki to ta Kasance Annamimiya Ce Kuma Makaryaciya.
-Wadda Kuma Ta Kasance da Surar Kare, lta Kuma ta Kasance Mai Hassada Ce.
-A ƙarshen Hadisin Sayyida Fatima (SA) Tace Azaba ta Tabbata ga Matar da ta Fusatar da Mijinta.
-Ni’ima Ta Tabbata ga Matar da ta Yardar da Mijinta.
-Allah Kayi Mana Tsari da Wadannan Munanan Azaba.
Aminu Abubakar