SHAWARA/KIRA GA MABIYA SHEIKH ABDULJABBÃR DA SAURAN MASOYA
DAGA BAKIN KWARARREN LAUYAN KARE HAKKIN DAN ADAN
(Barrister Ibrahim Garba Carefor) Assalamu Alaikum Warahmatullahi
Yan Uwa mutanen Dr, Abduljabbãr Kabara ya kamata Mutane Susa Zuciyar su a sanyi akan Wannan Hukuncin da aka yanke,na Farko ya kamata kusani a Tsarin mulki na kasa da kuma Tsarin Tafiyar da kotuttuka na kasa Wannan Kotu ta shari'ar Musulumci ta Sarki Ibrahim Yola batada hurumin yankewa wani Hukuncin kisa Kuma Hukuncin ya tabbata Tsarin Mulkin kasa Yana Gaba da duk wata Kotu ta customary ko wadda ake Kira ta shari'ar Musulumci magana na abinda ya Shafi na blasphemy kwata~kwata baya daga Cikin abinda za'a iya yankewa Mutum Hukuncin kisa Hukunci irin wannan,
Wanda Yake Mutum yanada dama ko a Jihar kano akwai kotuttuka Guda biyu wadanda za'a iya daukaka Kara Kuma akwai Babbar kotun kasa wadda akwai dama ta daukaka Kara wadda Tsarin Mulkin kasa yaba Dr. Abduljabbãr
So in akabi Wannan Hanyar za'asami nasara saboda Haka Mutane su kwantar da Hankalin su Wannan abin ma kamar Ina kallon shi kamar ma Zan Kira shi Kamar Wasa ne bazai taba yiwuwa ba,Kuma Mutanen Dake a Cikin Tafiyar ya kamata Susa Zuciyar su a sanyi Kuma a Guji Yin zage~zagen Abubuwa da Suka Shafi Gwamnati ko Suka Shafi wasu hukumomi ayi amfani da tantagaryar doka ma'ana shine dama ta daukaka Kara da akaba Dan Adam a Cikin Tsarin Mulkin Kasar nan Kuma wannan damar tabbatacciyar dama ce wadda babu abinda zai iya kankare ta sannan Maganar wani Hukunci wanda zai dauki Rai wadannan kotuttuka na Tarayya Sunada Adadin irin laifuffukan da Za'a iyayima dan Adam Hukuncin da Za'a iyayima dan Adam Akan laifin da yayi da zai iya daukar ranshi saboda Haka Inaso Jama'a su kwantar da Hankalin su Kuma Suyi abinda yadace su cigaba da Adduo'i su Saurara abita Hanyoyin da yadace na doka a daukaka Kara Kuma in an daukaka Kara Ni inada tabbacin Za'ayi Nasara
Wassalamu Alaikum
Rubutawa
Bun Ibraheem Abu Muhammad
+2347036969347