[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Hukumar Hisbah a Kano da ke arewacin Najeriya ta bayyana dalilan da suka sa za ta fara kama wasu 'yan matan da ke tallace-tallace a kan titunan jihar bayan faɗuwar rana.
A ranar Laraba ne Hisba ta ba da sanarwar fara kamen tana mai cewa bincikenta ya nuna cewa da yawan 'yan matan kan ɓige da karuwanci a cikin birnin da zarar dare ya yi.
Gwamnatin Kano ta ƙirƙiri rundunar Hisbah ne da zimmar kawar abin da ta kira baɗala da kuma tabbatar da mazauna jihar, waɗanda akasarinsu Musulmai ne, sun bi dokokin Shari'ar Musulunci.
Cikin ayyukanta har da hana shan giya, da kame matasa masu yin aski irin na mawaƙan Turawa ko kuma yin kitso da sauransu.
A ranar Talata dakarun Hisbar suka kama matasa kusan 20 bisa zargin su da haɗa bikin 'yan luwaɗi a birnin na Kano yayin da suke tsaka da biki, a cewarta.
Akwai irin wannan runduna a kusan dukkan jihohin arewa maso yammacin ƙasar, waɗanda akasarinsu Musulmai ne.
Babban Kwamandan Hisba a Kano Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya shaida wa BBC Hausa cewa binciken da suka yi ya nuna cewa 'yan matan da ke talla na aikata abubuwan ɓata tarbiyya idan dare ya yi.
"Idan suka zo tallan, kamar yadda bincikenmu ya nuna, sai su ajiye kayan, sai kuma su ci kwalliya, su shiga gari don su yi aikata abubuwan masha'a," in ji shi.
Ya ce za su dinga yin kamen ne da dare kuma ba su da niyyar hana tallace-tallace a birnin.
"Mun tura masu bincikenmu sun gano mana, wasu bayanan ma ba za su faɗu ba na irin ƙazantar da muka gani a irin waɗannan wurare."
Kwamandan wanda malami ne, ya ƙara da cewa zuwa yanzu suna kan matakin gargaɗi ne tukunna, inda suke jan kunnen iyaye.
"Muna yi wa iyaye gargaɗi da ke turo 'ya'yansu daga nan cikin gari ko kuma daga wajen gari cewa su ja hankulan 'ya'yan su daina kaiwa dare domin kuwa idan abin ya ci gaba to za mu kama su kuma doka za ta hau kansu.
"Haka nan idan muka tashi kamawa ba iya su kaɗai za mu kama ba, har waɗanda suke mu'amala da su.
'Da a ce iyaye sun san abin da ke faruwa za su haƙura da tallan'
Akasarin masu tallan kan shiga birnin Kano tun da farar safiya don kai kayayyaki da suka ƙunshi abinci, da goro, da mai na girki, da rogo, da zogale, da sauransu.
Sukan shafe tsawon yini kafin su koma gidajensu da yammaci.
Kwamanda Ibn Sina ya ce wasu daga cikin abubuwan da suka gano ba za su bayyanawa ba saboda girmansu.
"Idan za mu faɗa musu abubuwan da nake cewa ba za su faɗu ba, wallahi gara su haƙura da tallan a kan abin da za a janyo wa iyayen da jihar da al'ummar Musulmi," kamar yadda ya bayyana.