Anna Zalnci Shaikh Zakzaky da Almajiran sa.
Da misalin karfe 10:30 na daren Asabar 12/12/2015, sojojin suka kai hari gidan Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky da ke unguwar Gyallesu, inda suna zuwa suka fara bude wuta kan mai-uwa-da-wabi, tsawon wannan daren zuwa wayewar garin Lahadi ba tare da kakkautawa ba, inda a ranar Litini suka kama Shaikh Zakzaky da matarsa bayan sun kashe mutum fiye da 1000 a tsakanin gidan nashi da kuma Husainiyyah.
Daga cikin mutane kimanin dubu da sojoji suka kashe a Waki’ar Zariya, akwai ‘ya’yan Shaikh Zakzaky guda uku; Hammad, Humaid da Ali Haidar wadanda aka Shahadantar da su a gabansa, sai kuma dan yayansa mai suna Shamsudden da kuma yayar Shaikh din ‘yar kimanin shekaru 70 mai suna Malama Fatima (Guggo Binta).
Har ila yau, a waki’ar Zariya, sojoji sun shafe wasu gidaje ta hanyar kashe ‘yan gidan gaba daya, ko kuma wasu adadin ‘yan gida guda. Daga cikin irin wannan gidajen akwai Malam Abbas Abdullahi da sojoji suka kashe shi tare da ‘ya’yansa guda shida, har yau ba labarin ko da gawarwakinsu!
Wasu gidajen da sojoji suka kashe musu iyali a yayin kisan kiyashin Zaria sun hada da; Gidan Injiniya Yahya Gilima rai 5, gidan Malam Abubakar Zaki rai 4, gidan Dakta Isa Waziri rai 4, Dakta Mustapha Umar shi da ‘ya’yansa uku, haka ma Malam Yakubu Okene, shi da ‘ya’yansa uku, da sauran gidaje masu yawa da suka rasa mazaje, ‘ya’ya, ko iyayensu a yayin wannan harin.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Abbas a ranar Litini 11/4/2016 ya bayyana a gaban kwamitin binciken kisan kiyashin Zariya (JCI) da gwamnatin jihar ta kafa cewa, jami’an gwamantin jihar Kaduna ciki har da shi kansa da daraktan harkokin addini na jihar da kuma wasu Sanatoci, sun yi zama da gwamna Elrufa’i suka shawarta yadda za su bizne gawarwakin wadanda sojojin suka kashe a Zariya.
Alhaji Lawal Balarabe yace, bayan hakan sun je asibitin koyarwa ta jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) suka kwaso gawarwaki 156, sannan suka je depot din sojoji da ke Zariya suka kwaso wasu gawarwakin guda 191, jimilla 347 duk na ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky da sojoji suka kashe a Zariya. Wanda suka tafi da su kauyen Mando da ke bayan garin Kaduna, da taimakon sojoji 40, bayan da suka kirga gawarwakin a gaban Manjo-Najar Odundare, suka bizne dukkansu a ramin bai daya cikin dare.
Har yanzu gwamnati shekaru biyar kenan tana tsare da Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenah a kurkuku bisa zalunci, tare da cewa ko mutum daya daga soji ba a hukunta ba tun bayan Kisan Kiyashin nan.
Anya kuwa Allah zai kyale wannan al'amarin ya tafi a kawai?
Sauke Wannan