@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Kankana nau'in tsiro ne na furanni na dangin Cucurbitaceae 'ya'yan itacen da ake ci. Tsire-tsire mai Ban Sha’awa kuma mai kama da itacen inabi, 'ya'yan itace ne da ake nomawa sosai a duk duniya, tare da fiye da iri 1,000.
Amfanin kankana goma 12 ga jikin bil'adama.
Kankana na daya daga cikin ababen gona na marmari dake da matukar amfani ga bil'adama. Kankana wata aba ce mai dauke da ruwa mai zaki kuma mai amfani matuka ga jikin bil'adama. Masana sun bayyana Kankana da ‘ya'yan itaciya mai matukar amfani ga rayuwar bil'adama, don sindarai da ke cikinta na Vitamins, Minerals, Antioxidants, da kuma Calories. Wasu daga cikin alfanun Kankana goma sha biyu su ne:
1, Kankana na dauke da sinadarin dake samar da kariya da rage barazanar cutar hawan jini ga jikin bil'adama (Hypertension)
2, Kankana na taimakawa matuka wajen rage yawan kiba da nauyin jiki mai cutar da bil'adama.
3, Kankana na dauke da sinadarin “Glutathione” wanda ke taimakawa wajen kwarara garkuwar jikin bil'adama.
4, Kankana na dauke da sinadarin “Lycopene” wanda yake dagargaza kwayoyin cutar daji (Cancer)
5, Kankana na dauke da sinadarin (Vitamin C) wanda ke da tasiri wajen kashe kwayoyin cutar da ke cikin jinin bil'adama.
6, Kankana na dauke da sinadarin “Potassium” wanda ke taimaka wa zuciya, koda, Huhu da sauran muhimman sassan jikin bil'adama.
7, Kankana na samar wa fatan bil'adama kariya daga illolin da haske da tsananin zafin rana.
8, An bayyana masu shan Kankana da wadanda cutar Asthma za ta yi wuyar kama su saboda sinadarin Vitamin C da Kankana ke da shi. (Asthma prevention)
9, Kankana na taimaka wa jikin bil'adama wajen narkar da abinci cikin tsari.
10, Kankana na samar da kariya da rage barazanar cutar sugar ko Diabetes.
11, Kankana na samar da kariya ga cutar ciwon zuciya (Heart Attack).
12, Kankana na taimaka wa ma’aurata da kuzari da nishadi musamman a yayin gabatar da ibadan aure. Allah Yasa Mudace...