Amfanin 'Bawon Kankana...!!!


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 

 KARMU YADA BAWON KANKANA YANA DA MATUKAR AMFANI GA LAFIYA.

Mun saba idan muna shan kankana yayinda muka gama shan wajen jan mukan yada bawon ko mu bayar a dabbobi, toh idan ma kanayi ka daina domin kuwa binciken masana kimiyyar tsirrai sun tabbatar da amfanin sa ga jikin dan Adam, kamar dai yanda Luis pons ya rubuta a 21 ga watan Fabarairun 2003.

Kamar yanda binciken (Agricultural Research Service study) ya nuna, Luis yana cewa binciken ya tabbatar da cewa shi bawon kankana wajen korennan yana dauke da sinadarai irin su citrulline da amino acid da suke matukar taka rawa wajen taimkawa zagayen tsarin fitsari na jikin dan Adam, yayinda yake cire sinadarin nitrogen daga cikin jini ya taimaka masa wajen maidashi fitsari.

Har wa yau shi wannan bawo yana dauke da mafi karancin calories (ma'aunin dake dad'a kuzari ajikin dan Adam ko dabba), da kuma mafi yawan sinadarai masu kara Vitamin C, Vitamin A, Vitamin B6, Potassium, zinc da dai sauran su.

Ba iya nan ya tsaya ba haka kuma yana taimakawa ga abubuwa kamar haka:

1. Kiyaye fata:

Sabida sinadarin lycopene da kuma flavonoids da yake dauke dashi sai ya zamana yana taimakawa fata wajen hanata yankwanewa, tsagewa da kuma yana hana ko riga-kafin fitowar kurajen fata, ya na hana bushewar fata, da kuma dusashewarta, da kuma hana bayyanar alamun tsufan fata.

2. Yana rage blood pressure:

Kamar yanda yake dauke da sinadarin potassium dayawa hakan hasa yakan taimaka wajen rage stress wanda hakan yakan kare zuciya daga heart attack, stroke (borin jini), da kuma dattin zuciya.

3. Taimakawa Ma Su Hawan Jini:

Yawan shan kankana musammam bawonta na taimakawa mutanen da ke fama da hawan jini wajen saukar sa. Kamar yadda mu ka bayyana a sama daga cikin sanadaran da kwallon kankana ke kunshe da su akwai 'vitamins, niacin, folate, thiamine, vitamin B6 and pantothenic acid. Wadannan sandarai na taimakawa ma su hawan jini ta hanyar inganta hanyoyin jini.

4. Yawan shan kankana musamman bawonta na sanya rauni ko wani ciwo da mutum ya ji ya warke cikin gaggawa.

5. Karfin mazakuta:

Kara dankon aure tsakanin ma’aurata, sakamakon kara karfin mazakutar namiji da zai samu damar gamsar da iyali. Binciken zamani ya tabbatar da cewa Sinadarin 'Arginine' da ke kunshe cikin kankana na kara karfin maza kamar yadda magungunan kara karfi na zamani ke yi. Dan haka amfani da bawon kankana a takaice kan taimakawa Ma'aurata wajen kara ni'imar aure.

6. Gyaran Gashi:

Sanadaran Protein, Iron, magnesium da copper na daga cikin muhimman sanadaran da ka iya kiransu abincin gashi. Ita kuma kankana Allah Ya hore ma ta wadannan sanadarai ma su yawan gaske a cikinta. Saboda haka ne yin amfani da kankana akai-akai da tare da bawonta kan inganta lafiyar gashi, musamman ma ga matar da ke fama da zubewar gashi.

Kamar yadda binciken ya nuna, sanadarin 'Protein' na kara yawan gashi, shi kuma 'magnesium' yana hana zubewar gashi, yayain da shi kuma sanadarin 'Copper' ke ƙara sheki da yalyalin gashi.

7. Yawan shan kankana tare da bawonta na kara inganta lafiyar Koda

8. Daga cikin amfanin bawon kankana ga lafiyar dan adam, akwai kare mutum daga hadarin kamuwa da ciwon daji.

9. Maganin Gyambon Ciki (Ulcer):

kamar yadda mu ka ambata a farkon wannan makala, daga cikin amfanin kankana ga lafiyarmu har da maganin olsa wato gyambon ciki. Idan mutum na son amfanuwa da kankana wajen maganin gyambon ciki, sai ya ke shanta tare da bawon kullum da safe kafin ya ci abinci.

10. Shan bawon kankana na rage hadarin kamuwa da ciwon zuciya.

11. Saurin Murmurewa Daga Lafiya: 

Lokacin da mutum ya warke daga wata rashin lafiya da ya yi, idan ya juri amfani d kankana jikinsa zai yi saurin farfadowa.

12. Yawan Shan Kankana da bawonta na taimakawa mutum ya samu isasshen barci.

13. Kara Karfin Garkuwar Jiki:

Kamar yadda bincike ya nuna kankana na kunshe da sanadarin Vitamin C, wanda ke kara karfin garkuwar jiki, sakamakon haka sai ya kare jiki daga kamuwa daga cututtuka.

Wannan sune wasu daga cikin amfanin kankana da bawonta ga jikin dan Adam, sai a daina jefar da bawon kanka yan uwa. A amfana da maganin da yake dauke dashi. 

Allah Yasa Mudace...... 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post