AMFANIN TUBA:-Kurarran da mutum yake yi a Rayuwa, suna sabbaba masa Tambo a Zuciya. Da Duhu da Kunci na Tsiya...!!




Kurarran da mutum yake yi a Rayuwa, suna sabbaba masa Tambo a Zuciya. Da Duhu da Kunci na Tsiya. 


 Gurbataccen Tunani, Aiki mara kyau, Karar da Lokaci wajen Badala da Sharholiya, zama da Mutanen Banza, Rashin kulawa da Iyali ko Makwabta ko Aminai, Kaushi da Zafi a Mu'amalah, Banna da Al-mubazzaranci, Saba Al-kawali da Cin Amana. Duk wadannan Dalilai ne dake yiwa Zuciya Rauni, wanda ke zama Tambo bayan Nadama da Tuba. 


Tambaya a nan itace,  Shin Allah ya bar mana wannan Tabon ko Tambon ne,  domin ya tuna mana da Asarar da muka yo a baya,  domin mu yita zama cikin Kunci da Daci, domin mu dinga ganin kanmu a Wulakance cikin Al-ummah?  Ko kuwa ya bar mana su ne domin su tuna mana Ni'imarsa a garemu, mu kara Gode masa. Domin cincintar sabuwar Ni'imah. 


Duk wanda ya tafi a kan ra'ayin farko, to zai karar da Rayuwarsa ne cikin Dimuwa,  ba zai amfani Kansa ko Al-ummarsa ba. 


Wanda ya rungumi ra'ayi na biyu kuwa,  Shine Mai iya ginawa bayan Rusawa, Mai gyarawa bayan Batawa, Mai hadawa bayan Tarwatsawa, Mai Saitawa bayan karkatarwa. Shine wanda ya fahimci Falsafar da ke tattare a cikin Tuba da neman Yafiya. 


Babbar Hikimar Tuba,  shine bada dama ta biyu ba Nadama kawai ba. Tunawa da Rahamar Allah da Jinkansa yana karuwa bayan Tuba. 

Babu wata hanya ta maganin matsalolin Damuwa kamar Tuba, da Istigfari. 



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post