An dai gurfanar da Kabara a gaban kotu kan lamarin da ya shafi kalaman batanci ga Manzon Allah (SAAW) matakin da ke iya tada zaune tsaye A watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da shi
Abduljabbar dai ya bayyana gaban kotun cikin nutsuwar da ba’a taba gani ba tun bayan fara shari’ar yana mai ban carbi tare da sauraron karar
Da aka tambaye shi ko yana da wani abu da zai fada wa kotun Barista Aminu Ado Abubakar wanda ya tsaya a matsayin lauyan wanda ake kara, ya roki kotun da ta yi wa wanda ake tuhuma sassauci domin ya aikata abin da ya aikata bisa rashin sani
Sai dai Abduljabbar ya mike yana fadin bai san lauyan ba kuma shine karon farko da ya fara ganinsa
Ban san shi ba Wannan shine karo na farko da nake ganinsa Kada a bar shi ya yi magana a madadina Zan iya kuma ya kamata a bar ni in yi magana da kaina in ji Abduljabbar
Sai dai alkalin yace kotun ta amince da lauyan a matsayin wanda zai kare shi
Ku zartar da hukuncinku kuma ba ni neman sassauci ko kadan. Ina so dukkan mabiyana su sani cewa zan mutu a matsayin jarumi kuma ba na son kai (Alkali) Ibrahim Sarki Yola ka yi min wani adalci ko ka yi min sassauci Wannan ita ce maganata ta karshe Assalamu Alaikum
Abduljabbar ya ci gaba da cewa Ya mai shari’a bayan na ji yadda ka karkatar da dukkanin hujjojina kuma sai ka juyar da duk abin da na yi a kai, ka sanya min wasu kalmomi da ban taba furtawa ba
Hakan ta sanya alkalin kotun ya bayar da umarnin a huta na tsawon mintuna 20 kafin yanke hukuncin.