Alakali Ya Yankewa Ibnul Kayyem Hukuncin Kisa Sabo Da Yayi Ridda!!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Daga Shehul Islami Aminu

Ya wajaba Salafawa da ƴan korensu su sani shifa Tarihi maimaita kansa ne yake, saboda haka a duk lokacinda wata qadiya ta faru yanzu zaka tarar wani cikin Ƴan baya ya haɗu da irin wannan abin ɗaya faru gareka koda waninka da kake jiɓinta.


Bayan Kotun son Rai ta yanke hukunci irin na son rai, ɓataccen hukunci Aqlan wa naqlaan, sai wasu Salafawa suka shiga shirme da banbami irin nasu akan wannan hukuncin, sai dai kash mafi yawansu rashin sanin abinda ya faru akan Jagororin Mazhbarsu ko Founders nata yasa suke wannan abin, a rubutun daya gabata na kawo muku yadda ta kaya da Babban Jagoran nasu Ibnu Taimiya da yadda ƙarshensa ta kasance mutuwa cikin kurku, toh shima Khalipansa Sarkin yaƙinsa Ibnul Qayyem ku biyoni domin kuji kaɗan daga cikin irin hukuncin da Alƙali ya yanke masa saboda Aqidarsa.


DALILIN KAMA IBNUL QAYYEM NA ƊAYA.


Kamar yadda wasu Malaman Tarihi suka faɗa cewa 👇

وفى سنة 725هـ خرج ابن القيم حاجًّا، وأثناء عودته عقد درسًا للوعظ والتفسير بالمسجد الأقصى، تكلم فيه عن مسألة الزيارة، وشد الرحال لزيارة قبر الخليل بفلسطين وأنكرها؛ فهاج عليه الناس وثاروا، ورفعوه إلى قاضي القضاة؛ فحكم بردته وقتله


A shekarar 725 ce Ibnu' Qayyem ya fita yana mai nufin aikin Hajji, akan hanyarsa ta dawowa ya ƙulla Majilisi domin wa'azi, Tafsiri a Masallacin Qudus, inda a cikin Majalisin ne yayi magana akan Ziyarar Manzon Allah S A W da kuma ɗaura Sirdi domin tafiya ziyar ƙabarin Annabi Ibrahim A.s ya musa waɗannan ayukka, anan ne mutane suka motsa akansa suka zabura suka afka masa, suka kamashi suka kaishi inda alƙalin Alƙalai, anan ne Alƙalin Alƙalai ya yanke masa hukuncin fita Musulunchi tareda bada Umurnin a K*SHESHI.


Wannan shine abinda ya faru da Ibnul Qayyem, Babban Muridin Ibnu Taimiya. 


BAYAN KAMA IBNU TAIMIYA


Ga yadda ta kasance ga Khalifansa Ibnul Qayyem, Bayan kama ibnu Taimiya da yanke masa hukunci, kamun Babban Almajirinsa Ibnul Qayyem ne ya biyo baya, sai aka kama su Ibnu Kaseer, Burzaaliy, Katbiy da wasunsu., 


وكان لابن القيم النصيب الأوفر؛ إذ ضرب بين يدي القاضي والأمير، وأهين بشدة، ثم حمل على حمار مقلوبًا، وطيف به في أنحاء دمشق كما يفعل مع السراق والمفسدين، ثم ألقوا به في السجن مع شيخه ابن تيمية، ولكن بصورة انفرادية، وظل رهين حبسه حتى مات شيخه ابن تيمية  


Ibnul Qayyem yanada rabo cikakke a cikin waɗanda aka kama daga cikin Almajiinsa ibnu Taimiya, Saboda an zaneshi, an dakeshi anyi masa Buloli a gaban Alƙali da Sarki, Aka Wulaqantashi wulaƙanci mai tsanani, sannan aka ɗauke shi akan "JAKI" fuskarsa tana dubin bayan Jaki ( Fuskarsa na dubin bayan Jaki, Bayansa na dubin gaban Jakin) aka zagaya dashi a hakan bisa Jaki ko ina cikin sassan Garin Dimishqa, kamar yadda akewa Ɓarayi da Maɓarnata, sannan aka jefashi Kurkuku tareda Malaminsa Ibnu Taimy, sai dai a daban ba wuri ɗaya ba cikin gidan yarin, haka Ibnul Qayyem ya wanzu a gidan yari har Shehinsa Ibnu Taimiya ya mutu.


Ga kaɗan daga cikin Littafan Tarihi da za a koma domin ganin waɗannan Labaran tarihin 


• الدرر الكامنة: (4/ 21).


• البدر الطالع: (2/ 113).


• المختار المصون: (184).


• البداية والنهاية: (14/ 252).


• تراجم أعلام السلف: (695).


• ذيل طبقات الحنابلة: (20/ 448).


• شذرات الذهب: (3/ 168).


• النجوم الزاهرة: (10/ 249


العقود الدرية"، ص: 345


Jama'a wannan shine irin wulaƙanci, cin zarafi, keta alfarma, kama karya, ƙasƙancin da akawa Babban Almajirin Ibnul Taimiya, Malam, Ibnul Qayyem, to wanda akawa wannan abin tun shekara ta 725 shine yau Hijira ta 1446 zai zo saboda an zalunci wani yazo yana murna, sun mance sune ka kaf a tarihin musulunci aka fara yima wannan tuhuma ta keta Allah SWT, Manzonsa SAW, Sahabbansa, Matansa da Bayin Allah Nagartattu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post