[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
Akwai wani rubutu da yake yawo a kafafen sadarwa, wanda ake danganta shi ga wani Babban Malami da muke matuƙar girmamawa da yi masa fatan alkhairi , wai ance ya ce : Abinda ya hanashi bayyana kansa a matsayin ɗan Shi'a ko shiga Shi'a , shine yadda yake ganin wasu ruwayoyi a litattafan Shi'a, sai maruwaicin yace daga Imam Ja'afar Assadiƙ ya ruwaita, alhalin akwai tazarar shekara ɗari tsakaninsa da Imam Ja'afar Assadiq (a.s.) ɗin .
Wannan shi ya bashi tsoro da al'amarin Shi'a har yaƙi yarda da kansa a matsayin ɗan Shi'a .
AMSA :
Tare da dukkan girmamawa ga wannan Babban Malami mai daraja , idan muka yi rangwamen karɓar maganarsa a matsayin shubha, za muce masa :
1. Indai wannan ne abinda yasa ka ƙi zama ɗan Shi'a, to irin sa ne dai ya kamata ya hana ka amsa sunanka na Musulmi , domin kuwa ba iya cikin Littafan Shi'a kawai ba , har a Littattafan sauran ɓangarorin Musulmi akwai irin wannan , Babu wani ɓangaren Musulunci da babu irin waɗannan ruwayoyi , kenan in hakan zai sa ka guji Shi'anci shi yafi cancanta yasa ka guji Musulunci baki ɗayansa ,(La Samahallah) .
2 . In ta tabbata ka ga irin hakan a cikin Littattafan Shi'a ɗin kamar yadda kayi da'awa, to ba komai ake kiran wannan a wajen Malaman Hadisi face Hadisi Mursali ko Marfu'i (المرسل / المرفوع) , kuma ga duk wanda ya karanta Ilmin sanin mazajen ruwaya (علم الرجال) , yasan akwai Babi na Musamman da Malamai suke tattauna batun irin waɗannan Hadisai da Ruwayoyi da Aathar , kai har littattafai an rubuta akansu sukutum , kamar Al-maraasilu na Ibnu Abi Haatam da waninsa .
Hadisi Mursali yana daga rabe-raben Hadisi mai rauni , kuma ba hujja bane (ba'a aiki dashi ) a wajen Kunzumin Malaman Hadisi , indai mutum ya karanta ilmin Hadisi yasan hakan , tun a Irin su Littafin Baiƙuniyya , Alfiyatul Suyudi , Alfiyatul Iraƙi , Nukhbatul Fikr da Muƙaddimatu Ibnus Salah , za'a koya masa hakan kuma yasan hakan .
Misali ; Muslim bin Hajjaj yana faɗa a Muƙaddimar Sahihinsa (صحيح مسلم) yana cewa :
وَالْمُرْسَلُ مِنْ الرِّوَايَاتِ فِي أَصْلِ قَوْلِنَا وَقَوْلِ أَهْلِ الْعِلْمِ بِالْأَخْبَارِ لَيْسَ بِحُجَّةٍ "
Na'am , akwai Malamai dayawa (Fuƙaha'u) na Ahlussunna Wal jama'a da suka tafi akan halascin aiki da hadisi Mursali , Misali Annawawi a sharhin da yayiwa Sahihu Muslim yana cewa :
هَذَا الَّذِي قَالَهُ هُوَ الْمَعْرُوفُ مِنْ مَذَاهِبِ الْمُحَدِّثِينَ وَهُوَ قَوْلُ الشَّافِعِيِّ وَجَمَاعَةٍ مِنَ الْفُقَهَاءِ . وَذَهَبَ مَالِكٌ وَأَبُو حَنِيفَةَ وَأَحْمَدُ وَأَكْثَرُ الْفُقَهَاءِ إِلَى جَوَازِ الِاحْتِجَاجِ بِالْمُرْسَلِ "
Ya bayyana saɓanin da akai akan aiki da Hadisi Mursali, kuma ya bayyana ɓangaren da suka yarda da Hujjiyarsa , kamar Maliku da Abu Hanifata da Ahmad, da kuma waɗanda basu yarda da ita ba , kamar su Mallam Shafi'i.
Hakanan wasu Malaman Ahlussunna Wal jama'a sunyi togaciyar Marasilun wanin Tabi'ai kamar Sa'idu Bin Musayyib , sukan samawa Marasilun sa mafita saboda since daga Sahabbai yake rawaita kai tsaye , su kuma Sahabbai dukkansu Adilai ne , kamar yanda aka danganta wannan ra'ayi ga Mallam Shafi'i.
To kusan haka yake a wajen Malaman Shi'a, a dunƙule Maraasilu suna daga Hadisai masu rauni ba'a aiki dasu , amma anyi togaciyar wasu Maruwaita da Malamai , kamar su Ibnu Abi Umair (Ashabul Ijma'i) , da Sheikh Assaduuq idan yayi amfani da harshen Ƙala (قال )ba Ƙiila (قيل ) ba , saboda wasu dalilai da an ambacesu a Muhallinsu , to ana karɓar Maraasilunsu a wajen Malaman Hadisi da Fiqhu na Shi'a.
3. Yana da kyau wannan Malami yasani ; Akwai abinda ake kiransa Mashyakha(مشيخة) a wajen Malaman Hadisi na Shi'a , wani salo ne da suke amfani dashi wajen rawaito Hadisi, ta yanda sukan shafe sunayen Maruwaita daga Isnadi yayin rubuta Hadisi , sai su tafi can ƙarshen Littafin ya rubuta sunan Maruwaitan a tsare , ko su rubuta hanyar da suka samu littafi ko wani ɓangare na Isnadi da suka zabtare , shi yasa za'a ji ana cewa Mashyakhar Assaduuq ko Mashyakhar Aɗɗusi , Misali .
Sheik Assaduuq yana da Maraasilu dayawa kuma yana da Mashyakha shi yasa Malaman Hadisi suka ƙulla Babuka da Fasulla akan hukunci da bayanin yadda al'amarin Maraasilun sa suke .
To , wanda bai san Shi'anci ba kuma bai yi karatun sanin Shi'anci bane , daga ya ga irin wannan (Ruwaya ba Isnadi ko an yanke wani ɓangare na Isnadin ) , sai ya ruɗe yaga kamar mai rauni ce ko karya ce in bai bincika Mashyakhar sa ba .
4 . Matukar abinda dai za'a iya jifan irin wannan Hadisai da Malam ke magana shine rauni, to amma ai ba duk Hadisi mai rauni bane bashi da amfani kwarai-kwata , tayu Hadisi bai inganta ba amma ayi aiki dashi ko a fai'idantu dashi ta wasu fuskoki kamar hikma ko wa'azi ko ƙarfafar masu inganci ko karinoni a cikinsa , tayu Hadisi ya inganta amma kuma ba za'a ayi aiki dashi ba saboda wasu illoli da dalilai , uwa uba akwai wata Ƙa'ida da ke Kiranta Kai'idar Rangwame a cikin dalilan Sunnoni (قائدة التسامح في أدلة السنن) , da(أخبار من بلغ) shima wani karatu ne anan mai zaman kansa.