@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
“Ina son in jajanta mana dangane da abinda mu ka gani ya faru da ɗan’uwammu Shaikh Abduljabar Allah Ya bashi kariya Ya kubutar da shi Ya bashi istiƙama na zalincin da aka yi masa. An zalince shi ba kaɗan ba to amma dai ɗaukakar matsayi ne a wajan Allah Ta’alah. Ko ma minene ya faru, ya samu fita? a’a bai samu fita ba? duka dai ɗaukakar matsayi ne a wajan Allah Ta’alah babu hasara a cikin wannan magana, kasuwanci ne da babu hasara a ciki sai dai riba kuma an yi da yawa ya faru, kuma an yi da yawa bai tabbata ba (dan haka) ba hasara a ciki.
A cikin ruwayar Ahlulbaiti (A.S) na cewa: “Alƙatalu lana ada wa karamatuna indallahi Shahada”. (ma’ana) kisa gare mu al’ada ne. Kisa ga Ahlulbaiti da mabiyansu al’ada ce, ɗaukakarmu kuma matsayi gun Allah Shahada. To ka ga idan ya zama haka ai mutum bai da hasara ko misƙala zarratin sai dai ba zai hana a ambaci zalincin azzalumi ba duk da ya ke akwai wasu mutane wanda Allah Ta’alah Ya faɗa a cikin Alkur'ani mai girma ya na cewa:
وَلَقَدْ ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرًا مِّنَ ٱلْجِنِّ وَٱلْإِنسِ ۖ لَهُمْ قُلُوبٌ لَّا يَفْقَهُونَ بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لَّا يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ ءَاذَانٌ لَّا يَسْمَعُونَ بِهَآ ۚ أُوْلَٰٓئِكَ كَٱلْأَنْعَٰمِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ ۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلْغَٰفِلُونَ.
To ana samun wannan kowane jinsin na mutane har a cikin Musulmi. Waɗannan ma su kiran kansu musulmi da su ke ɗaukar irin wannan matakin kamar abinda aka yi wa Malam a Zariya? wanda shugaban ƙasar ya na kiran kansa musulmi, mukarrabansa wasu da yawa musulmi ne da sojojin da farar hular duka galibin su musulmi, da shi abinda ya faru a Kano da gwamnan da sauran malamai da abinda ya faru a Kaduna, Elrufa’i da makamantansu galibinsu za ka ga duk musulmi ne. To ba ruwan Allah akwai wasu mutane da Allah Ya halicce su dan jahannama dan su shiga wuta ne kawai.
In banda haka nan ka je ka kashe mutum haka kawai ba dalili saboda tunaninsa ko aƙidarsa tare da cewa kuma mutum ya yi rantsuwa cikin rantsuwar nan ta sa hada kiyaye jinanan mutane, zai kiyaye mutane zai kiyaye addininsu, rayuwarsu, jinanansu, dukiyoyinsu ba tare da banbancewa ba to rantsuwar da su ke yi kenan cewa ba maganar son zuciya kowwa ɗaya ne da wanda ya zaɓe su da wanda bai zaɓe su ba za su kiyaye jinanan mutane da addininsu sannan kuma ƙarara an rubuta a cikin ‘constitution’ cewa:
Kowwa na da ’yancin ya yi addinin da ya ga dama wato ma’ana duk yadda ya fahimci abinsa madamar bai shiga haƙƙin wani ba to ba dalilin da za a tsangwame shi bilhasali ma a bashi kariya kuma aka ce addinin nan ko da zai yi ne shi kaɗai ko da jama’a ko a sarari ko a ɓoye duk ya na da wannan dama ɗin wannan haka ya ke rubuce cikin tsarin mulkin da su ka rubuta.
Sannan kuma babu inda aka ce sai fahimta kaza za a yi babu inda aka ƙayyade, yanzu misali a ce ba a yarda ka bi mazhabar Ahlulbaiti ba ko Mazhabar Shi’a to ita kuma Mazhabar salafiyya wa ya kawo ta? In ka ce nan mu ai ba shi’a ba ne, to mu kuma ba salafawa ba ne. Dama asalan mu salafawa ne? Addini da salafiyyanci ya shigo mana? to me ya sa salafawa su ka shigo su ka miƙe ƙafa su kuma? Idan Shi’a ba za ta shigo ta miƙe ƙafa ba dan me salafanci zai zo ya miƙe ƙafa shi kuma, me ya sa?
Idan an ce kuma ai mu asalimmu malikawa ne sai mu ce wane nassi ne na alƙur’ani wanda ya wajabta wa mutane sai mazhaba kaza za ku yi? babu. Babu wata aya ko hadisi da ya ce mazhaba wane za ku yi bilhasali ma Manzon da ya zo da musulunci (S) bai san Maliku ba, bai san Shafi’i ba, bai san Abu hanifa ba, bai san Ahmad ibn hambali ba, amma ya san da zaman Imamu Jafarus-Sadiq (A.S).
Dan daga cikin wanda ya lissafa khalifofinsa har da (Imam) Jafarus-Sadiq da kuma hadisi sahihi na Sunnah ba na Shi’a ba, saboda haka kaga idan kace kai Jafariyyah ne to kai ke yin mazhaba da lasisi Saboda ka dogara da Imam Jafarus-Sadiq ɗaya daga cikin jikokin Manzon Allah 12 da ya bari, wanda duk ba wannan ba to ‘illigal’ ya ke yi ba ta da stamp daga Annabi.
Ko mutum ya yarda ko kar ya yarda haka ya ke in an je lahira ya gani ko haka ne ko ba haka ba ne in nan duniya ya na jayayya, ballantana kuma karya su ke yi sun sani saboda ya na rubuce ingataccin malamansu sun sani sun rubuta haka nan ne sun tabbatar da haka nan ne, saboda haka inadi ne da girman kai da son zuciya umayyaci ne, umayyanci ne ya motsa na abinda su ka yi wa Ahlulbaiti shi ne har yanzu ya ke jan gezarsa ga masoyansu ko mutum ya so ko ya ƙi wannan abu iyakarsa kenan in banda haka miye dalili?
Yanzu idan na bi Ahlulbaiti miye laifin me na yi ma ka? nai ma wa laifi ne? wace doka na karya, ta majilisar ɗinkin duniya, ta ƙasa, ta addini, ta gargajiya, wace doka na karya? In kuma har na karya doka ne? me ya sa wanda ya zo da salafanci shi bai karya doka ba?...”
—Shaikh Yakub Yahya Katsina a jawabinsa kan haramtacciyar shari’ar da aka yi wa Shaikh Abduljabar Nasiru Kabara Kano, ya yi jawabin jim kaɗan bayan kammala karatun juma’a (23/12/2022) na Arba'una Hadith na Imam Khomaini (Q.S).
Cigaban jawabin na zuwa...
#SYYK
24Dec2022