Tun yana matashi ya fahimci da'awar Shaikh Zakzaky(H), kuma bai taba gazawa ba wajan baiwa wannan harka gudummawa ba ta kowane janibi. Wallahi Malam har tausayi yake bani idan naga yadda yake gudanar da rayuwarsa. Wannan bawan Allahn ya sadaukar da dukkanin lokacinsa ne ga harka, domin ban taba ganin ya fifita maslaharsa akan ta addini ba.
Ta bangaren kiyaye lokaci kuwa, na tabbatar al'umma zasu masa wannan shedar, koda program aka gayyaci Malam, to lallai a sa ran ganinsa dai-dai da lokacin da'a fada masa (sai dai idan wani uzurin ne ya gitto masa). Malam yana yawan tunatar da yan uwa dangane da muhimmantar da lokaci da tsara al'amura.
Dangane da ibada kuwa shi samfur ne ga yan uwa. Malam yana yawan horon yan uwa musamman matasa dangane da kusantar Allah ta hanyar ibada. Sannan Malam yayi kokari wajan kyautata alaka a tsakanin yan uwa da sauran mutanen gari.
Tabbas, samun irinsu Malam a matsayin Uba a cikin al'umma babban baiwa ce ga al'umma, tsayuwarsu kuwa a harkar addini babban nasara ce da cigaban al'umma wajan saituwa bisa kyakykyawar hanya.
MALAM JUNAIDU MUHAMMAD SANI (Wakilin yan uwa na Kudan), Allah Ya girmama ladan ayyukanku, Ya jagoranci al'amuranku,Ya kara muku kusanci, Ya saka muku da Aljannah madaukakiya.
Babu wani abu wanda aka fadi akan wannan bawan Allah wanda yake ba hakan bane, illama se dai nace an rage wasu cikin halaye ko kokarin nashi. Muna fatan Allah ya tsawaita rayuwar shi, ya kara mishi lafiya.
ReplyDelete