[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
—Bin Yaqoub Katsina.
Wani abin al’ajabi ya faru a ranar Talatar da ta gabata (13/12/2022) a cikin garin Katsina inda gobara ta ci ta cinye wani gida amma cikin ikon Allah ta tsallake jaridar nan ta Almizan wadda kamfanin ‘Mizani Publications’ ke bugawa mai fitowwa duk sati, tare da Mujallar jirgin tsira ta Katsina wadda ke fitowwa lokaci bayan lokaci.
Wannan abu dai ya faru ne a gidan wani tsohon ɗan jarida da ke zaune a rukunin gidajen ‘Mocage Gate’ da ke kallon gidajen Fatima Shema a cikin birnin Katsina. Wani babban abinda ya ja hankalin mutane shi ne yadda wutar ta cinye komai a gidan amma da ta zo kan wannan jarida ta Almizan da mujallar Jirgin tsira, sai ta ci gefe-gefe ta wuce, duk da kau jaridar ta almizan ma wani feji ne kawai a ciki ba dukanta ba.
Da ma dai ma su wannan jarida sun sha faɗa a rubuce cewa; a riƙa yi mata kyakkyawan riƙo, kada a riƙa wurgar da ita ko yin ƙulle-ƙulle da ita kamar zuba ƙosai ko nama, domin akwai sunan Allah ciki da sauransu. Haka kuma ita ma Mujallar jirgin tsira domin ita dama duk abubuwan da ke cikinta sun danganci Manzon Allah (S) da iyalan gidansa tsarkaka ne kawai.
Hakan dai ba baƙon abu ba ne domin ya sha faruwa a duk sadda Allah ke son ya nuna wata ƙudira da ikonsa, a kan wani abu mai muhimmanci da daraja, musamman wanda ya shafi addinin Musulunci.
MediaForumKatsina
18Dec2022