Abduljabbar ya karantawa alkalli hakikanin yadda auren Nana safiya ya kasance

 


DR SHEIK ABDUL JABBAR KABARA YA KARANTAWA ALKALI HAKIKANIN YADDA AUREN NANA SAFIYYA YAKASANCE A ZAMAN KOTU NA RANAR 17_3_2022


 Malam Ya Cigaba Da Cewa Wani Abu Da Zai Tabbatar Da Ita Kanta Qissar Ta Auren Nana Safiyya Kirkirarta Akayi,


Duk Sun San Cewar Kafin Khaibar Da Shekara Biyu Aka Aureta, Wato Kamin Ayi Waki’ar Da Akace An Kamota A Cikin Bayi Ta Kasance Matar Manzon Allah (SAW) Kuma Hatta Bukhari Ya Kawo Cewar Da Ita Akaje  Yakin Usfan, Kuma Idan Muka Duba Cikin.


         “AL AHADU WAL MASANIY”


Na Ibn Abi A'sim Mujalladi Na 5 Shafi Na 440 Yana Tarjamar Hadisan Matan Ma’aiki Yazo Kan Nana Safiyya Wacce Tazo A Tarjama Ta 1069 Sai Ya Kawo Tatsuniyoyi Marasa Kyau,

Amma Sai Gashi Ya Kawo Hakikar Auren A Mujalladi Na 6 Shafi Na 112 Tarjama Ta 1208 Karkashin Hadimar Ma’aiki Mai Suna “Amatullah” Ga Yadda Auren Ya Faru: Daga Bakin Amatullah Wacce Itace Yar Kuyangar Da Ma’aikin Allah Ya Bawa Nana Safiyya A Matasayin Sadakin Ta A Lokacin Da Ya Aureta,


Ga Yadda Ta Fadi Ainihin Yadda Akayi Wanna Aure Mai Albarka 


   Amatullah Tace Annabi (SAW) Ya Ribaci Nana Safiyya A Yakin Banu Kuraiza Ya Bata Sadakin Babata


A Duba “Musnad Abi Ya’ala” Mujalladi Na 6 Shafi Na 170 Tarjama Ta 7125 Wanda Shi Ya Kawo Cikacciyar Qissar Kuma Itace Mafi Girmamawa Ga Hakkin Ma’aikin Allah,


Ga Yadda Amatullah Tace Babarta Razina Ta Gaya Mata Ma’aiki Ya Ribaci Nana Safiyya A Yakin Banu Kuraiza Da Nadir,

Da Nana Safiyya Taga Yawan Bayin Da Aka Kamo Sai Tayi Kalmar Shahada,

Sai Annabi Yazo Da Ita Yana Janta Da Hannunsa,

Sannan Yazo Da Ita Ya Nemi Aurenta Ta Amince,

Sannan Ya Bata Sadaki.


Sannan Malam Ya Fara Kawo Litattafan Da Suka Kawo Yadda Auren Na Gaskiya Ya Kasance Kamar Haka


1___ A Duba “ATTAUDIH” Sharhin Bukhari Amma Basa Kawo Ta A Gurin Nda Ya Yamata,

Amma Idan Aka Duba Mujalladi Na 25 Shafi Na 227 Bayan Duk Bayanan Da Yayi Sai Yace Ibn Mandah Da Wasunsu Sun Tabbatar An Bata Sadaki Da Kuyanga Mai Suna “RAZINA”

Amma Sai Ya Cire Qissar Da Take Nuna Ba A Khaibar Akayi Ba.


Malam Yace: Daga Wadanda Suka Fadi Auren Nana Safiyya Na Gaskiya Akwai


2___ “Dabariy” Mujalladi Na 24 Shafi Na 277 A Mu’ujamul Kabir Nasa. Yace Ma’aiki Ya Bata Sadaki Da “RAZINA” Kuma Ya Tabbatar Da Dalilin Yantata Shine Kalmar Shahada Da Ta Fada. 


3___ “IBN ASAKIRA”  Mujalladi Na 2 Shafi Na 221 Yayi Tarjamarta Bai Fadi Yadda Akai Auren Na Gaskiya Ba,

Amma Sai A Mujalladi Na 4 Shafi Na 325 Sannan Ya Kawo Cikakken Auren Wanda Ya Hada Da Sharadin Auren Na Gaskiya Wanda Ya Gabata A Baya.


4___ “UMDATUL KARIY” Juz’I Na 20 Shafi Na 15 Ya Kawo Yadda Akayi Auren Na Gaskiya.


5___ “HASA'ISUL KUBRA” Ta Baihaki Juzu’I Na Takwas Shafi Na 209 Ya Kawo Maganar Gaskiya.


6___ “BIDAYA WAN NIHAYA” Ta Ibn Kasir Ya Kawo Auren Na Gaskiya Saidai Tarjamarta Daban Bayanin Auren Shima Daban A Duba Mujalladi Na 5 Shafi Na 307.


7___ “SUBLUL HUDA” Na Salihi Shima Ya Kawo Cikakken Auren A Mujalladi Na 7 Shafi Na 213.


8___ “USUDUL GABA” Ta Ibnl Asir Mujalladi Na 7 Shafi Na 21 Ya Kawo Gaskiyar Auren Cewar Anyi Sadaki Da Komai. 


9___ Abu Nu’aim Shima Ya Kawo …...

 

A Nan Ne Alkali Yace

“A BARSHI HAKA KADA NA KASA KARANTAWA”.


Anan Gurin Sai Malam Yayi Tanbihi Game Da Irin Munanan Ruwayoyi Da Ake Nasabtawa Ma’aikin Allah Tare Da Tabbacin Maruwaita Akan Sam-Sam Kir-Kirarru Ne,


Kuma Wannan Shine Irin Tambayar Da Yan Jarida Suka Yimin


Wai Me Yasa Nake Fushi Idan Ina Karanta Irin Wadannann Zantuttuka 

Nace Abinne Yake Da'muna Matuka

Domin Ganin Mafi Yawan Maruwaita Sun San Abinda Suke Nasbtawa Annabi (SAW) Tatsuniyoyine.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post