A Zamanin Wani Sarki Da Ake Kira Haruna Rasheed Ko Kuma Abu Jaafar, Anyi Wani Mutum Da Ake Yi Masa Ganin Mahaukaci Mai Suna Bahlu.

 



Watarana Wannan Mutumin Yana Zaune Akan Wani Kabari Sai Ga Sarki Haruna Rasheed Ya Zo Wucewa Ta Wajen Tare Da Dogarawansa, Ya Kalli Wannan Mutumin Yace: "Ya Kai Bahlu! Ya Kai Wannan Mahaukacin!

.

Wai Yaushe Ne Zaka Yi Hankali?.

.

Sai Bahlu Ya Sauka Daga Kan Kabarin Ya Koma Kan Wata Doguwar Bishiya Dake Gefen Kabarin Sannan Ya 'Daga Murya Sosai Yana Cewa:

..

"Ya Kai Haruna ! Ya Kai Wannan Mahaukaci ! Yaushe Ne Zaka Yi Hankali?".


Fadawa Suka Fara Muzurai Duk-Da Sun San Mahaukaci Ne Akan Zasu Suburbude Shi,

.

Sai Sarki Haruna Rasheed Ya Hanasu.

.

Sai Sarki Haruna Rasheed Ya Zaburi Dokinsa Yaje Karkashin Bishiyar Da Bahlu Yake Yana 'Daga Kansa Yace: "Yanzu Kai Bahlu, Da Ni Da Kai Wanene Mahaukacin?

.

Kai Da Kake Zama Akan Kabari


Ko Kuma Ni?".


Bahlu Ya Ce: "Ina ! Ai Ni Ina Da Hankali Na"

.

Haruna Rasheed: "Ta Yaya Kuwa Haka Zata Kasance?"

.

Bahlu: "Sai Ya Nuna Yatsarsa Sama Ya Nuna Wasu Gine-Gine Na Fadar Sarki Haruna Rasheed Sannan Yace: "Saboda Ni Na San Wadancan Gine-Ginen Masu

'Karewane, Shirme Ne Kawai,

.

Amman Wannan Kabarin Shine Tabbas Shi Yasa Nake Raya Shi Kuma Na Dawo Shi Yasa Na Raya Shi,

.

Kai Kuma Sai Ka Ruguza Naka Kabarin Ka Gina Benaye a Duniya,

.

Shi Yasa Baka Son Zuwa Inda Naka Yake Domin Ka Riga Ka Ruguza Shi".

.

Bahlu Ya Cigaba Da Cewa: "To Yanzu Sai Ka Fada Min Wanene Mahaukaci Tsakanin Ni Da Kai?".

.

Sarki Haruna Rasheed Yayi Kuka Sosai Har Sai Da Gemunshi Ya Jike Da Hawayen,

.

Sai Yace: "Wallahi Ka Fadi Gaskiya Ya Kai Bahlu, Ina Son Ka Karamin Wani Wa'azin".

.

Sai Bahlu Yace: "Ai Littafin ALLAH Qur'ani Ya Isheka Wa'azi".

.

Sarki Haruna Rasheed Yana Jin Haka Sai Yace:"Ya Kai Bahlu Kana Da Wata Bukata Da Kake So In Biya Maka Ne?".

.

Sai Bahlu Yace: "Kwarai Ma Kuwa, Bukatuna Guda Uku Ne Kacal:

.

1. Ka 'Kara Mini Shekaru Na A Duniya

.

2. Ka Kare Ni Daga Mamayar Mala'ikan Mutuwa

.

3. Ka Saka Ni a Aljannah, Ka Nisanta Ni Da Wuta.

.

Sarki Haruna Rasheed Yace: "Wallahi Ko 'Daya Ba Zan Iya Biya Maka Bukatun Naka Ba".

.

Sai Bahlu Yace: "To Ka Sani Cewa Wallahi Kaima Kanka Abun Mulka Ne, Kai Ba Mai Mulki Ba Ne, Don Haka Ka Sani Bani Da Wata Bukata A Wajenka, Bukatuna Duka Suna Wajen Mai Mulkin Sammai Da 'Kassai".

.

LA'ILAHA ILLALLAH........

.

Ya ALLAH Kasa Makwancinmu Bayan Mun Koma Gare Ka Ya Haskaka, Mu Kuma Samu Yalwa Da Sukuni A Cikin Shi. AMEEN.

.

Katura Wannan Sakon Ga Yan Uwa Musulmai Domin Su Amfana

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Masha Allah naji Dadi sossai ga wanna wa'azi

    ReplyDelete
Previous Post Next Post