14 Ga Disamba! Ranar da tafi kowace rana baƙinci.

 



A irin wannan rana da suka ritsa da shi, bayan duk sun karar da mataimakansa sun kame na kamewa, sun ƙone saura. Da wanne zai ji?

Da kishin ruwan kwanaki biyu da suka sha?

Ko da hayaƙi da zafin wutan kona gidansa da aka yi?

Ko da bude masa wuta yana tare da ya'yansa, da aka tsaya ya ga ashe an fille wuyan dansa da harsashi, an tarwatsa kan dayan ta goshi da harsashi shima?

Jagora zai ji ne da ganin Haidaar yana duba fuskan kannensa yana cewa Abbah sun kashe su, nima ka bar ni na fita su kashe? Amsa masa zai yi ko shiru? Da me Jagora zai ji, a yayin da yake ganin Ali Haidar wanda shi ya rage idanmasa a wannan wajen ya fita, sun bude masa wuta sun fasa kansa, ya fadi, sun dauki gawarsa sun wurga ta wani gefen?



A yayin da Shaikh Zakzaky ke kokari toshe idanunsa da mai da kwayar idonsa bayan an fasa masa da harsashi. Zai ji ne da hannunsa da ya yi yunkurin dagawa ya ga a karye yake har kashi ya bulluko a ragargaje? Ko da kafarsa wacce suka dagargaza da harsasai?

Me ya kai quna da zafin a gabanka a cirewa matarka da ta san kimar hijab hijabinta? Abbanmu zai ji ne da cire Hijabin matarsa Malama da soja ya yi, ya ja ta ya fitar da ita yana mata izgili, alhali Jagora ko kallonta ya kasa a wannan yanayin?

Dattijo dan shekaru 65, basu ji nauyin su ja jikinsa a kasa ba bayan sun jika kayansa da jini. A kokarin su masa izgili suka ja shi a kasa suka jefa shi a baro suna waka da rawa akan sun kawo karshen Shi'a a Nijeriya.

Da ace ba a jefi Annabi (S) an fasa masa kai, da ba a masa rotsi an zubar masa da hakora, da ba a jikkata shi da harbi a Uhudu ba, da ba a yanke kan Annabi Yahya an ba karuwa ta yi rawa da shi a kasuwa  ba, da ba a yanke kan Imam Husaini (AS) an tsire an rika masa izgili ba, da ba a cire Hijabin Iyalan gidan Annabi a Karbala ba, da ba a kashe Annabawa 70 a rana daya an saka su a rijiya an rufe an cigaba da cin kasuwa ba, da duk wadannan abubuwan da aka wa Jagoranmu sun girgiza imaninmu. Amma Alhamdulillahi yin wadancan da masaniyarmu a kai, sun tabbatar mana da cewa lallai Jagoranmu yana bisa tafarkin Allah da Annabawa da Salihan bayi.


Alhamdulillah.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post