Daga Ibraheem El-Tafseer
A wannan rana ta 12/12/2015 ce, a yau shekaru Shida kenan cif, kwambar Sojojin Nijeriya, ƙarƙashin Buratai da Kuka Sheƙa, bisa umarnin Janaral Buhari suka auka wa almajiran Shaikh Zakzaky a Zariya, jihar Kaduna. A wannan rana an yi abin da ba a taɓa yiwa wani irin sa ba a Nijeriya.
A wannan rana ta 12/12/2015 Sojojin Nijeriya sun kashe almajiran Shaikh Zakzaky sama da dubu (1,000), sun ƙona wasu da ransu, sun bizne wasu da ransu. Har jarirai basu tsira ba a wannan rana. Sun yi kisan rashin Imani a kan raunana waɗanda basu ɗauke da ko da Allura da sunan makami.
Sun rushe Husainiyya, Fudiyya Islamic Center, Darur Rahama da gidan Shaikh Zakzaky, wai duk an yi haka ne domin kawo ƙarshen Shi'a a Nijeriya. Kowa yana da 'yancin ya yi addini yadda ya fahimta, amma banda ɗan Shi'a. To hakan ya kawo ƙarshen Shi'a Nijeriya?
An kashe wa Shaikh Zakzaky zaratan 'ya'yansa guda uku a gabansa, an harbi matarsa, shi kuwa harbin kisa suka masa, Allah ne ya raya shi. Guraguzan harsasai ne a jikinsa yau shekaru shida, amma an hana shi ya je Asibiti don neman lafiya. Sun riƙe passport ɗinsa.
Suna jin haushin an kaisu ƙara Kotu, Kotun ta bada umarnin a sake su, shi da matarsa, a biya su diyya, amma gwamnatin Nijeriya ta ki bin umarnin Kotun. Daga ƙarshe dai dole suka sake su bayan kotun ta wanke su tas daga dukkan abin da ake tuhumarsa da shi
Allah ya karbi shahadar shahidanmu, ya gaggauta ɗauka mana fansar jinanensu, ya ƙara wa Shaikh Zakzaky da Malama Zeena lafiya tare da dukkan 'yan'uwan da suke tsare, ya gaggauta wulaƙanta Buhari, Elrufai, Buratai da duk mai hanu a waki'ar. Bi haqqi Sayyida Zahra (SA).