12 ga december 2015. Ranar da Buhari ya yunkurin Kauda Harkar Musulunci a Najeriya.

 


Wannan Wani Rubutu ne Da Saifullahi M. Kabir yayi Tun  A 2021 Cikar Waki'ar Zariya Shekaru 6.

Shafin Ma'asumah Nigerian News Update, Ya Dawo muku dashi

----

Yau 12 ga December, shekara 6 cur da yunkurin gwamnatin Buhari na shafe Harkar Musulunci da Jagoranta daga doron samuwa. Amma Alhamdulillahi, Allah Ya qi yarda, ya wanzar da rayuwar Jagora da cigaban Harkar Musulunci.





Sojoji sun yi barnar da suka Shahadantar da fiye da mutum dubu a Zaria a cikin kwanaki biyu kacal, suka kona wasu, suka kashe mata da yara da tsofaffi, suka tattara duk gawarwakin suka je suka haka ramummuka suka bizne su a ramin bai-daya.


A tsawon shekaru shidan nan, azzaluman mahukuntan kasar nan sun yi iyaka kokarinsu na ganin sun wargaza Harkar Musulunci ta kowace hanya, ta karfi da ta hanyar ruwan sanyi, amma albarkacin tsayuwar Jagora da wasu yan uwa da suka tsaya suka dake, suka rika nuna musu yatsa a ko wane lokaci, wannan nufin bai yiwu ba, har gashi ya tabbata yanzu cewa gwamnati ta fadi warwas!


Baya ga mutum dubun da Sojoji suka kashe a Zariya, daga waki'ar zuwa yanzu, jami'an tsaro sun kashe mutane kusan 180 a garuruwa daban daban a yayin tarurrukan yan uwa da muzaharorinsu. Sun kama mutane dubbai, amma bisa ikon Allah a yanzu suna tsare da mutanen da ba su wuce 60 bane a Kurkuku tun daga 2019. Duk yan uwan da jami'an tsaro suka kama suka kai kotu, kotu ta wanke su ta sake su a tsawon lokacin nan.


Wannan rana ce ta jinjinawa Shahidai da Gwarazan gwagwarmaya da suka dake, aka jijji musu ciwo, aka kakkama su aka tsare, aka Shahadantar da wasu, da kuma wadanda duk da dakewar tasu Allah bai kaddara musu ko daya daga cikin wadannan ba, da ma wadanda suka tsayu da kokarin sauke wazifarsu a kowane bangare a wannan Harkar. Allah Ya kambama ladanku, ya saka mu a danshinku.


Wannan rana ce ta jinjinawa Shahidai da Gwarazan gwagwarmaya da suka dake, aka jijji musu ciwo, aka kakkama su aka tsare, aka Shahadantar da wasu, da kuma wadanda duk da dakewar tasu Allah bai kaddara musu ko daya daga cikin wadannan ba, da ma wadanda suka tsayu da kokarin sauke wazifarsu a kowane bangare a wannan Harkar. Allah Ya kambama ladanku, ya saka mu a danshinku.


Mu da muka kasance masu rauni, hakika ni da ire-irena, wallahi na sani duk sadda aka yi batun tsayuwa ko sadaukarwa, ina daga cikin gazazzu, muna rokon Allah Ya yafe mana, ya sanya mu daga cikin masu gyara kuskuren baya da aiki a gaba. Ya bamu ikon cin jarabawar gaba. Ya azurta mu da kyakkyawar karshe ta Shahada.



Kamar yadda Jagora (H) ya ke ta nanatawa, cewa Waki'ar Zariya ta rubutu a zukatanmu, kuma za ta rubutu a takarda ko allon da ba zai taba goguwa ba ilal-abad! Ina kira ga duk masu baiwa da kokarin ganin wannan ya tabbatu ta kowace hanya, kan mu yi kokarin hakkakar da hakan da ayyukanmu.



Allah Ya sakawa Jagoranmu da dukkan alkairanSa, ya girmama ladansa a kan girman jarabawowin nan wadanda shine farko a shansu kafin kowannenmu. Allah Ya cigaba da iya masa. Ya bashi lafiya da kariya.


— Saifullahi M Kabir

12/12/2021



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post