Zuwa ga almajiran allamah Ibraheem Zakzaky Hafizahullah.

 


Cikin girmamawa nake roƙon wanda yaga rubutun nan ya tsaya ya karanta don sanin halin da bayin Allahn nan ke ciki.

Bayan Fitowar su daga Kotu ranar Larabar 24/11/2021 Mai Shari'a Chikere bata zo Kotu ba aka ɗage shari'ar zuwa wata biyu, kuma saura wata ɗaya Alƙaliyar tayi Ritaya kenan shari'ar su zata koma baya, tun lokacin nayi tunanin yin rubutun nan don tunatar da 'yan uwa nauyin dake kan mu.

***********************

YAUSHE AKA KAMA SU? WACE TUHUMA AKE MUSU?

An fara kama Mallam Ibrahim Husaini ranar Alhamis 28/02/2013 a gidan sa Kaduna.

Bayan sati biyu suka kama Mallam Haruna Abbas shima ranar Alhamis 14/03/2013 a filin Jirgin saman Kano.

Sai Mallam Adamu Sulaiman ranar Litini 16/06/2014 a wurin sana'ar sa Legas.

Bayan gallaza masu da gana masu nau'o'i na azaba tsawon lokaci, Jami'an leƙen asiri na ƙasa (DSS) sun gurfanar dasu a Federal high court Abuja ranar 06/11/2014 Court 7 daga baya ta zama Court 6 gaban Mai Shari'a Ademola 

Ana tuhumar su da aikata ta'addanci. 

Sau uku Turawa daga Isra'ila suna zuwa cikin Kotun Alƙali ya tashi su shiga Chamber ya dawo yaci gaba da Shari'a.

Bayan kwashe lokaci mai tsawo suna zuwa kotun daga wurin Dss, sunje sau 18 sai saɓani ya shiga tsakanin DSS da Alƙalin har suka kama shi, duk da yana cikin Alƙalan da suke ɗasawa don shi ya ɗaure Kabiru Sokoto da sauran su. Yana dawowa yace ba zaiyi shari'ar ba don haka su kai wata Kotun.

Daga nan suka maida shari'ar Court 5 Wacce ta zama Court 3 yanzu gaban Mai Shari'a Chikere

ta maida shari'ar farko. sun fara zuwa ne ranar 03/03/2017. 

An ɗauki tsawon lokaci ana shari'ar don sau 48 suna zuwa kotun, Dss sun gama kawo dukkan shaidun su, anzo yanke Hukunci babu laifi ko ɗaya da aka iya jingina masu, sai Dss suka ce suna da sauran shaidu don haka aci gaba da shari'a.

*************************

TAMBAYOYI GARE MU 'YAN UWA

1. Kenan babu wani mataki da zamu ɗauka? haka zamu yi shiru ayi ta azabtar da waɗan nan Miskinan?

2. Shin Mazlumiyyar su bata kai yin koda gangami a masallatai da markazozi ba?

3. Ina marubutan mu?

Yaushe zamu feƙe Alƙaluma wurin tallata wannan baƙin zaluncin?

4. Munyi Muzaharori a Abuja lokacin kama ma'aikaciyar Press TV Marzie Hashime, yaushe zamuyi koda a social media ne akan su?

5. Shin wai muna tuna su cikin sallolin mu?

6. Yaushe zamu yi zaman addu'a muyi kuka ga Allah don neman kuɓutar su?

7.Yaku 'yan uwa na masu daraja mutum nawa suka taɓa kai masu ziyara tunda aka mai da su gidan Yari?

8. Wannan azzalumar Gwamnatin bata iya ciyar da hatta waɗan suke tsare

Shin mun san yadda suke rayuwa? 

9. Dukkan su magidanta ne masu iyali wane irin tallafi muke baiwa iyalin su ta fuskar ci da sha, sutura, asibiti da Makaranta?

10.Mal. Haruna nada mata 2 yara 11.

Mal. Ibrahim Mata 1 yara 7.

Mal. Adamu mata 2 yara 4 da wasu marayu 4 dake hannun sa, 8 kenan.

Mu tambayi kan mu don Allah ya suke rayuwa?😭

Su ba iyalin Shahidai ba bare mu'assasa ta kula da su. 

Wai don Allah waye ke kula da su?

Ko da'irorin garuruwan su 

Haɗeja, Kano da Kaduna suna kula da su❓

Idan rubutun nan ya yi maka, ka taimaka kayi sharing har a samu canji a sabon shafin nan da aka buɗe.📖

26/11/2021

Shehu Al-ja'afaree Kaduna ✍️

#Reposted

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post