Idan baka da Aure kana cikin jarrabawa haka idan kanada shi kana cikin jarrabawa,


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 


Zaman Aure ibada ne ...gareku 'yan mata da samari babban kuskure da samari da yan mata musamman masu shiriyin Aure a wannan lokacin 75% sunayin Aure ne badan Allah ba. dayawan matasa suna biyewa rudun soyayya ne wajen yin Aure batare da sanin menene Aure ba . Yakamata kasamu ilimin zaman Aure kafin kayishi wannan shine zai baka damar cinye duk wata jarrabawa dazata bijiru maka bayan Aure. 

Tabbass Aure Akwai jarabawa acikinsa sosai, Idan baka da Aure kana cikin jarrabawa haka idan kanada shi kana cikin jarrabawa, 

Wani zaice tayaya wadda yake da Aure yake cikin jarrabawa????

 Tabbass shima yana cikin jarrabawa musamman idan baiyi sa'a samun abokiyar zama na gari ba ko tabayi ba. Tabbass rashin sa'ar abokin zama na gari babbar jarabawa ce ga rayuwar Aure, Saboda duk abinda zakuyiwa juna bazaku burge juna ba.
Tabbass wadda baida Aure yana cikin jarrabawa saboda kana ganinshi zaka ganshi baya cikin nutsuwa komai nashi babu tsari rayuwarsa tana cikin kunci wadda sai shi yasa abinda yake damunsa..karin maganar hausawa dasukecewa baza'a ji mutuwar sarki abakina ba. 

**YIN AURE SUNNA NE AMMA RIKESHI FARILLA NE** 

Abin sani gamasu Shirin yin Aure shine wasu malamai sukace idan har ka mutu bakayi Aure ba Allah bazai tambayeka ba . Amma idan kamutu kana da Aure Allah zai tambayeka yaya ka rayu tsakaninka da iyalanka shin kasauke hakki da Allah yace ka sauke.



- Ka samar musu da muhallin zama??
- Ka basu tarbiya ta addini??
- Ka basu ilimin??
- Ka dauki nauyi cinsu da shansu??
Da sauran duk wasu hakki da yahau kanka a tsakayinka na mai gida. Wajibine ka samar musu da duk wasu abubuwan da addinin ya wajabta maka a matsayinka na mai gida. 

**WAJIBINE MACE TAYIWA MIJINTA BIYAYYA**

Mace tayiwa mijinta biyayya wajibine idan bai saba umarnin Allah ba. 
- Wajibine tayi masa abinda yake so saboda umarnin Allah ne... 
- Wajibine ta tsare mutuncinta
- Wajibine ta kyauta ta masa
- Wajibine tabi umarninsa ta hanu da abinda ya haneta da sauran wasu hakki da yahau kanta wajibine ta sauke ..


 

**MUGINA RAYUWAR AURENMU SABODA ALLAH**

Tabbass duk rayuwar Aure da aka ginata ba saboda Allah ba tabbass rayuwar bazata jimaba .yin komai saboda Allah shine cin nasarar a rayuwa. Tun farko idan katashi yin Aure kasa a ranka cewa zakayi Aurene saboda Allah badan komai ba . tabbass idan kayi Aure saboda Allah...Allah zai taimakeka


Dayawan yaya mata basa samun damar cigaba da karatunsu bayan sunyi Aure komai yasa hakan yake faruwa?? laifin waye mijin daya Aureta ko iyayenta ko ita????

Ni anawa fahimtar duk suna da laifi saboda tunda farko idan mutum yazo neman Auran yarka idan kanada da bukatar tayi karatu zaka sanar masa cewa koda bayan auransu zata cigaba da karatu, Ta bangare mijinta kuda iyayenta basu fada maka sharadi kafin Aurenta ba hakine kabata ilimi addini dana zaman, Sai bangaren ta kuwa tabbass idan har takasace mai son karatun babu abinda zai hanaki cigana da karatunki koda bayan kinyi Aure. tabbass mace mai ilimi kowane da namji yake so ya Aure . Saboda mace mai ilimi ko azaman Aure ta babbata da wadda batadashi musamman idan akace maka ta hada biyu ma'ana tanada ilimin addini dana zamani. 

**MACE MAI ILIMI**

Mace mai ilimi itace zinariya a gidan mijinta itace garkuwa a wajen mijinta saboda zata kare dukkan wani hakkinshi akanta.
Masu iya mana nacewa mace mai ilimi Aljannar duniya, Mace mai ilimi garkuwa awajen yayanta, Kota bangare girki tasha banban da jahila.

Sanin kowane idan ka ilimantar da yar mace kamar ka ilimantar da dukkanin Al'ummane Mace mai ilimi ita zata bawa yayanta tarbiya ta gari. 



Sanin kowane yasan yadda akasarnan ake da karanci mata a bangare karatun aikin lfy wadda zaka gani abinda yan mace yakamata tayiwa yar uwatar mace saboda babu mace sai dai namiji yayi saboda karancin mata a wannan bangare. Kodan wanna ma yakamata mubasu dama suyi karatu idan sunada ra'ayi hakan.

Tabbass 'ya'ya mata sunada gudunmawa dazasu bayar acikin Al'umma idan sukayi karatu

Yakamata mubawa yaya mata suci gaba da karatu kobayan sunyi Aure.


SAEED MUHAMMAD SALEH... 
 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post