KUNDIN TARIHIN HARKA, dandali ne na yanar gizo da aka samar domin tattarawa tare da adana ta hanyar rubutawa, ji da kallo, da sauran abubuwan da ake iya gani na Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky domin buga su a zamanance (dijital).
Za a kaddamar da shafin na zamani ne a nan gaba kadan kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa hannun wanda ya fara gudanar da aikin, Ammar Muhammad Rajab, kuma aka rabawa manema labarai a Kaduna a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba, 2022.
A cewar sanarwar, dandalin na yanar gizon wani aiki ne da aka samar da shi ba don riba ba (nonprofit) da nufin adana tarihin Harkar Musulunci. “Har ila yau, shafin na yanar gizon aiki ne na sa-kai kuma ba shi da alaka ta kai tsaye ga jagorancin Harkar. Kawai mun bayyana ne da nufin bayar da ta mu gudummawar wajen ci gaban Harkar ta hanyar dijital,” in ji shi.
Sanarwar ta kara da cewa, "Manufarmu ita ce mu rubuta tare da adana duk wani abu da ya shafi Tarihin Harkar Musulunci tare da yadawa domin inganta hanyoyin samun bayanai game da Harkar a zamanance (wato ta hanyar dijital)", in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Burinmu shi ne mu zama wata ingantacciyar kafa wacce za ta zama tsani na fahimtar Tarihi, gwagwarmaya da akidun Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky.
Sanarwar ta kara da cewa, domin cimma wannan manufar da hangen nesan, “lokaci zuwa lokaci za mu rika gudanar da bincike kan batutuwa daban-daban da nufin tattara bayanai tare da buga su a wannan shafi. Haka nan muna iya ba da horo ga masu bincike domin inganta wadatar sahihan bayanai dangane da Harkar Musulunci a shafukan Intanet. Baya ga haka, mun shirya tattara bayanan da ake da su na harkar Musulunci tare da adana su a wannan shafin na intanet da aka samar,” in ji sanarwar.
Baya ga babban shafin yanar gizon, "shafin zai kuma kasance a shafukan sada zumunta kamar Facebook, Twitter, Telegram, YouTube, WhatsApp da dai sauransu," in ji sanarwar.