A wani mataki na taskace sahihin tarihi da fikirar Harkar Musulunci wanda Shaikh Ibraheem Zakzaky ya kafa, an rubuta wani kayataccen littafi, kuma tuni aka shirya kaddamar da shi.
Littafin matar Sheikh Ibraheem Zakzaky ce, wato Malama Zeenah Ibraheem ta rubuta shi.
A hirarta da tashar ABS Channel TV a Disambar 2021 Malama Zeenah, ta ce ta rubuta littafin ne saboda wasu abubuwa da ta ga yana faruwa na rashin fahimta da yada bayanan da ba daidai ba a lokacin da ake musu haramtacciyar tsarewa bayan kisan kiyashin da Buhari ya yi a Disambar 2015.
Ta jaddada cewa ta rubuta littafin ne a lokacin da ake musu haramtacciyar tsarewar nan daga 2015 zuwa 2021.
Wannan shi ne littafi na farko da aka rubuta kan takaitaccen Tarihin Harkar Musulunci daga wacce ta san Harkar.
Za a sanar da rana da wurin kaddamar da littafin a nan gaba.
*Sanarwa: Academic Forum, Sisters Forum da Mu'assasatu Abul-Fadl Abbas karkashin jagorancin Sayyeed Ibraheem Zakzaky (H)*