@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BUSHEWAR ZUCIYA KE SA IDANUWA SU BUSHE
Ma'anar bushewar idanu shine rashin jin kunyar Allah ko mutane yayin aikata abinda Allah yayi hani a kansa ko kuma wani abin zargi. Idan a kaga mutum na aikata abin zargi ko dukkan wani nau'in abubuwan da Allah ya hana, to, ana cewa wannan mutum idanunsa ya bushe.
To, menene ke jawo bushewar idanu? Za mu sami amsar wannan tambaya cikin wannan riwaya daga Imam Ali (A. S).
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع مَا جَفَّتِ الدُّمُوعُ إِلَّا لِقَسْوَةِ الْقُلُوبِ وَ مَا
قَسَتِ الْقُلُوبُ إِلَّا لِكَثْرَةِ الذُّنُوبِ[179].
Amirul-muminina (A. S) yace :
" IDANUWA BA SA BUSHEWA SAI DAI SABODA BUSHEWAR ZUKATA, KUMA ZUKATA BA SA BUSHEWA SAI DAI SABODA YAWAITA (aikata) ZUNUBAI. "
Cikin hadisin anyi amfani da kalmar wahaye 😢 (DUMUU'U) ne kinaya ga idanu, shi yasa muka fassara shi kai-tsaye da idanuwa.
Abinda hadisin ke nuna mana shine, duk wanda ka gan shi da bushewar ido, to, haqiqa bushewar zuciyarsa ce ta bayyana qarara a idanuwan nasa. Sannan kuma ba haka kawai zuciya ke bushewa/qeqashewa ba sai ta hanyar yawaita sabawa Allah. Kenan duk wanda ka gan shi da qeqasasshiyar zuciya, to, haqiqa munanan ayyukansa sun yawaita.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
25th May, 2022/ 25th Shawwal, 1443.