Sayeed Ibrahim Zakzaky (h) |
@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
Wanine yazo gun jikan ma'aikin Allah (s) sai yace, shin menene hakkokin musulmi kan musulmi"sai yace dashi, akwai hakkoki guda (7),Wajibabbu, wanda babu dy dg ciki face wajibine akan musulmi, Wanda yabar daya dg ciki, to yafita daga qarqashin yiwa Allah biyayya, bashida rabo dg kason bayi, Sai mutumin yace, Nakasance fansa gareku menene wannan hakkoki?
Sai jikan manzon Allah (s) yace, Lalle ina maijiyemaka tsoro, kada ka salwantar da rayuwarka akansu, kasansu baka kiyaye suba, Sai mutumin yace, babu Wani iko sai dg Allah(T)
Sai dan manzon Allah (s) yace:Hakkokin musulmi kan musulmi shine"
1,kaso ma dan uwanka dik abinda kaso ma kanka, tare d qimasa abinda kaqima kanka,
2,kaguji bacin ransa tare d son yardarsa d km bin umarninsa
3,Zaka taimaka masa, d qarfinka,dukiyarka,Harshenka, Hannunka, da qafarka.
4,Zaka zama Masa ganinsa, Madogararsa, Madubin dubawarsa.
5,Kada ka qosar d kanka shi y Kwana d yunwa, Ko ka qosar d qishinka Shi ya kwana d kishirwa, Ko ka suturtu shi y tsiraitu.
6,Zaka karbi rantsuwarsa, ka amsa qiransa, kaziyarci marar lafiyarsa, ka halarci jana 'izarsa.
7,Idan kasan cewa yana da buqata sai ka Hanzarta maganceta basai ka bari ya tambayeka hajarsaba, kaizaka Hanzarta rigashi ka magancemas.
To idan ka aikata haka, kajibintar da lamarin ka zuwa ga lamarinsa, Haka kuma ka hada soyayyar ka da nasa.
Allah yasa mudace🙏👏😘
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Tunatarwa