Ki kiyaye dukkan namijin da zai ce miki ki kawo masa ziyara a rayuwa, wannan ba mijin aure bane, fasiki ne kawai.
Ki kiyayi dukkan namijin da zai ce shi ba ya son zuwa hira anguwan ku wai sai dai ku haɗu a wata anguwan ko wani wuri, ba masoyi bane.
Ki kiyayi dukkan namijin da yake ce miki ba ki waye ba, dan iska ne, ya bari mana in ya aure ki ya wayar dake.
Ki kiyayi dukkan namijin mai miki hirar batsa a chatting, ko waya, ko text message, ko mai ce miki kuyi vedio call babu kaza da kaza, ko vedio call in dare.
Ki kiyayi dukkan namijin da yake taɓa miki jiki, domin yau ya taɓa miki jiki kika yi shiru gobe ma zai kara ke
macece da kika kai lokacin aure, kina da sha'awa ke ba dutse bane, ko yatsa ce namiji da ya taɓa miki dole kiji wani abu daga zaran kika fara barin sa to watarana kuwa za ki faɗa sabon ALLAH, wanda bai san dadin zuma ba labari yake ji, amma matuƙar ya fara ɗandana bai iya bari kuma zai fara sha yau da gobe, Kinga kenan za ki faɗa tarkon zina kenan, rabu dashi kawai ba wata uzuri.
Duk wanda yace yana sonki yaje ga iyayen ki sa'annan sanya yayan ki ko wani dan'uwa na gari bincikar halayyarwa wurin abokan sa, sau da dama wani zai ga yarinyar kirki amma burin sa mummuna ne akanta, rayuwa sai da ta-ka tsantsan.
Ki kiyayi shiga na banza, fifita soyayyar ALLAH da Manzon sa saw
akan na kowa, sai kuma soyayyar iyayen ki sa'annan malaman kirki, riki karatun Alkur'ani, hadis, dss, riko da sallah, azkhar, kina amfani da TUNATARWA na malamai, iyaye da kuma Mutanen kirki, ki wadatu da abinda ALLAH ya bawa iyayen ki sa'annan ki samu sana'a duk kankantar sa kina ɗan yi.
From Sistocinmu matanmu Group
By
Nucieyn Abbantah
(Ummu Ma'asuma)
Admins number
07062284589
08101234648
E-SISTOCINMUMATANMU@GMAIL.COM
ALLAHU YA KARAWA SU ABBA LAFIYA
Tags:
Kalaman Soyayya