Yadda Zaka Kare Kan ka Daga aikata Zinar Hannu, (Masturbation).

 

@MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE 




Wasu matasan mu da 'Yan mata' da yawan su sun daurawa kansu aikata zina da hannun su ta hanyar taba al-aura, haka yana yawan faruwa ne sakamakon rashin aure da wuri, da kuma ainahin ziyartan shafukan batsa...

Wannan mummunan Dabi'a ta MASTURBATION, tayi illah wa matasan mu sosai kusan yawancin matasan mu da mata sun kware wajan iya aikata shi, kuma yafi zina illah, Hanyoyi mafi shahara da binciken mu ya tabbatar mana game yadda ake aikata wannan mummunan Dabi'a kamar haka:-

1. Akwai wanda suke anfani da murya, mace tayi anfani da muryan Namiji ko dai Namiji ya yi anfani da muryan mace, ta hanyar kira ta cikin wannan sautin murya da yake fitowa tsakanin su na maganan batsa, ta haka suke fidda maniyyi...

2. wasu kuma su kadansu a cikin daki misali: Mace tana zaune ita kadai zata dinga shafa al-aurar ta, haka ma Namiji shima, ta haka suke biyan bukatansu.

3. Wadansu kuma ta hanyar kallon blue film... Banso na tsawaita bayani saboda magan-ganun suna da nauyi sosai gaskiya, Amma dai ina fatan an fahimta. 

Hakika wannan mummunan Dabi'a tana mugun cutar da rayiwa dan Adam, wasu daga cikin masu aikatawa sun san illar sa wasu kuma basu sani ba saboda a lokacin da kake aikatawa sam ba za kaga wani alama ba Amma dai abin yana cin jikin ka sosai a boye, kuma Idan ya fara bayyana kanshi a jikin ka a lokacin ya gama cutar da kai ya yi maka illah sosai' wani lokaci Insha Allah zan mana bayani game da illolinsa a jiki, da kuma irin yadda yake lalata sassan jiki.

SHAWARA A TAKAICE

Dole zaka haramtawa kanka shiga shafukan batsa, dole zaka kuji kallon duk wani abin da zai daga maka sha'awa, Dole zaka cire tinanin abubuwan a ranka na batsa, zaka guji wasa da macen da ba muharramanka ba, ka dinga shiga cikin mutane ka dena zama kai ka dai cikin Daki indai ba wai kana wani abu mai anfani ba, Babban maganinsa shine mutum ya yi Aure kawai, Babu wani magani daya wuce wannan, Idan babu hali sai ka luzumci yin Azumi

Saboda haka, matasa yan mata Aji tsoron Allah, wallahi Inda kun san illar wannan abin da ba zaku aikata ba.

Allah Ya tsaremu... 
       

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post