A yau Juma'a 25/11/2022, yara almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) 'yan kasa da shekaru 10 su gabatar da ƙwarya-ƙwaryar mauludin Manzon Rahama(S) a Kofar Arewa, Kudan.
Babban abin sha'awar shine, yaran sun dade suna tara yan kudadensu domin shirya wannan mauludi, inda suyi tattali su tara kudade masu auki, su gayyato malami ya gabatar musu da jawabi tare da abokanansu na makaranta da unguwa domin sharakawa.
Malam Muhammad Bakir Mika'il, shine ya kasance bako na musamman mai gabatar da jawabi, inda a cikin jawabin nasa ya jawo hankalin yaran dangane da al'amarin zuwa makaranta, fadin gaskiya, biyayya ga iyaye da sauran dabi’un Manzon Rahama(S). Sannan daga karshe ya bayyana jin dadinsa ganin yadda wadannan yara suyi wannan tunani na shirya mauludi dukda kasancewarsu masu kananun shekaru.
Daga karshe a gabatar da walima sannan ayi addu'a a sallami mahalarta.
— Abbakar Ibraheem Kudan
25/11/2022.
Shiga Nan Domin Kasancewa Damu a Shafin mu na Telgram 👇👇