YADDA AKA GUDANAR DA TARON ƘARAWA JUNA SANI NA SHIYYAR DAURA ƘARO NA FARKO.

 


Tun bayan faɗaɗa yankuna da I.M Production ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) ta yi wanda ake kira ZONING a turance, an ƙara samar da wasu yankunan, da ana da yankuna biyar (5) ne kaɗai sai aka ƙara fadada su zuwa yankuna tara (9) wanda a ciki  ciki harda Yankin Daura (Daura Zone); wanda ya haɗa da KAZAURE, DAURA, MASHI, MANI, DORO da kuma BAURE & BABBAN MUTUM.


Bayan fitar da wannan yankuna da I.M Production ta yi, an bayar da shawarar yin taron ƙarawa juna sani wanda wasun mu suka fi sani da mu'utamar a duk bayan watanni uku (3) a kowane yanki cikin yankuna guda tara (9) dake faɗin ƙasar.


To Allah cikin ikonSa dukkan yankuna sun ɗauki wannan muhimmiyar shawara kuma sun yi amfani da ita har ma sun gabatar da wannan taro mai muhimmanci. To su ma yankin Daura ba a bar su a baya ba.


A ranar Assabar 26 ga watan Nuwambar shekara ta 2022 sun gudanar da wannan taro karo na farko a garin ɓaure, in da taron ya samu halartar manyan malamai da kuma masana a ɓangarori daban-daban da suka shafi Samarwa ( wato, Production a turance).


An fara gudanar da taron ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe kuma an ƙarƙare da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.


Ga abubuwan da aka gabatar kamar haka:


1. Buɗe taro da Addu'a: Wanda ɗaya daga cikin Malamai ya gabatar.


2. Karatun Alkur'ani mai girma: Wanda ɗaya daga cikin Membobin I.M Production wato Khadijah Abdulwahab Daura ta gabatar.


3. Gabatar da Taro: Mal. Iliyasu Ƙarƙarku ne ya gabatar wanda ya wakilci Mal. Hamza Daura.


4. Ajin Acting: Malama Asma'u Daura ta gudanar da wannan ajin inda ta yi bayani sosai mai matuƙar muhimmanci ga mahalarta taro ma'anar Acting da kuma yadda ake yinsa.


3. Ajin Make-up (Kwalliya): Mal. M. Adam Kazaure tare da Malama Zahra'u Kazaure ne suka gudanar da wannan aji inda suka mana jawabi muhimmi game da kwalliya da yadda ake yinta a Fim, sun taɓo mana ɓangarori da dama a fannin kwalliya da yadda ake yiwa mutum rauni ko a fidda wani sashe daga cikin jikinsa.


Bayan an kammala wannan ajin na Make-up (Kwalliya) ne aka tafi hutu, an yi sallah sannan aka ci abinci kuma aka dawo.


Bayan an dawo a ci-gaba da gudanar da taron kamar yadda aka tsara, an gabatar da abubuwa kamar haka:


4. Gasar Tamsiliyya: An gabatar da gasar Tamsiliyya tsakanin garuruwa ukku (3) da suka haɗa da KAZAURE, DAURA sai kuma ƁAURE da BBM a matsayin rukuni guda. Wannan Tamsiliyya ta faɗakar ta ilmantar sannan ta nishɗantar da masu kallo, an fitar da wanɗanda suka yi na ɗaya da na biyu da kuma na ƙarshe kamar yadda yake a al'adar gasa.


5. Ajin Rubutu (Script Writing): Abubakar Abdu Daura shi ya gudanar da wannan aji, ya yi bayani ga maharta taro yadda za a maida labari zuwa labarin fim, wanda za a sa Ɗauɗauka (Camera) a ɗauka wato Screenplay kenan a turance.


5. Ajin Editing: Malam Yasir Haruna Daura ne ya jagoranci wannan aji, yayi bayani sosai a kan editing da yadda ake yinsa kuma ya kawo misalan Softwares ɗin da ake amfani da su wajen yin wannan aiki na editing. Ya faɗaɗa bayani sosai inda ya nuna cewa ko da babu komai da ya shafi fim, kama daga labari, kwalliya, Ɗauɗauka, da sauran su to edita yana da damar da zai iya haɗa fim shi kaɗai.



6. Jawabi kan Muhimmancin I.M Production ga ƴan harka Islamiyya: Malam Mustapha Muhammad Daura shi ya gudanar da wannan jawabi, ya yi jawabi mai matuƙar muhimmancin gaske ga ƴan uwa inda ya  fara da ma'anar  wannan forum na I.M Production da kuma hadafin da ya kafu a kai, Malam ya yi ƙarin haske game da yadda duniya ta ci-gaba sosai ta hanyar Fina-finai da kuma yadda saƙo yake saurin yaɗuwa ta wannan hanya.



Ba zai yiwu na naƙalto muku duk abin da Malam ya faɗa a wannan muhimmin jawabin na sa ba amma dai gaɓa mafi muhimmanci shi ne; ka sani, ki sani, mu sani, cewa Ibada muke yi kuma mu yi don Allah.


7. Jawabin Rufewa/Kammalawa: Malam Sadiq Ƙarƙarku ne ya ƙaƙare mana taron da muhimmin jawabi gamsashshe, ya faro mana tun daga farkon farawa ma'ana tun lokacin da Sayyid Zakzaky (H) ya fara wannan da'awa, abu ya gangaro ya taho har aka fara samar zauruka (Forum) har izuwa ita kanta I.M Production.



A taƙaice dai mun sha gwala-gwalan jawabai masu ƙarfafawa daga bakin Malaman mu masu Jawabi.


Sai Abu na Ƙarshe wato Rufe Taro da Addu'a: wanda Malamin mu kuma Baban mu, Amir na Garin Ɓaure ya kammala mana taron da Addu'a.


©Daura Zone I.M Production Media Team

Daga: A A Wisdom Daura


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post