Sheikh Zakzaky (H)
--------------------+---------------------
Ya ake son sayyada ZAHRA? Mata anan suna da wani al'ada kila har ynzu yana nan suna son su dauki garan Zahra. Shine son Zahra? Ko wake da rawa?
Ai gane masibar Zahra da kuka Dan masibar Zahra da bakin ciki Dan masibar da ya sami Zahra shine son zahra.
Imam Hussein (as) a ranar karbala a lokacin haduwar su da Hur bin yazid. Lokacin da aka fadi sunan sayyida Fatima sai Imam Hussein ya lura idanun Hur bin Yazid (Ra) ya kada hawaye ya gangaro yace tun a lokacin yasan shi mumini ne. Dan ba Wanda ainihin hawaye zai zubo masa daga idanunsa sanadiyyar musiban Zahra sai mumini.
Duk da gashi general ne na sojan yazid yazo ya tsare Imam Hussein amma Imam Hussein da aka fadi sayyida Zahra (s) sai yaga idansa ya kada sai yasan cewa to wannan mumini ne.
To kaga wannan ya nuna maka.. Ashe kaga yadda ake son sayyida Zahra kenan. Ana bakin ciki da bakin cikin ta ne. To sai ya zama kuma bakin cikin na ta an hanaka ka sani. wannan ba karamin zalumci bane. Da babbar mazlumiya har ma da Hausa akan CE a bugi mutum a hana shi kuka? Kasan in ka daki mutum yaji zafi ka zalunce shi in kuma yayi kuka kace Sam bazai yi kuka ba ka ga Karin zalunci kenan.
To wannan shine abinda akayi. Anyi zalunci akace Sam baza'a fada ba. Kuma ba ma.. Ku ma dole wadda sukayi aikin dole a wanke su ace mutanen kirki ne, ace ma sune addinin musulnci
To na'am ga dukkan girmamawa ga masu ra'ayi irin nasu. Tunda ance hatta ma da nassin alqurani an hana mu zagin wadanda masu bautan wanin Allah suke bauta ma , masu bautan wanin Allah idan suna bautawa wani abu an hanaka ka zagi abinda suke bautawa. La'alla gunki ne suka sassaqa karka zagi gunkin. Kana iya musu magana na hankali kace bazai yiwu wannan ya zama shine ubangijin da ya hallici sama da kasa ba tunda da babu shi daga baya aka same shi kuma ma ku kuka yi shi kuma ka nuna musu ta fuskan rashin cancanta da hikima da kyakyawan wa'azi.
------------------------------------------
--Sheikh Zakzaky (H) cikin jawabin sa na tunawa da shahadar sayyida Zahra (sa) rana ta 3 da yamma a cikin H-Baqiyyatulla Zaria.
~ Bin Isa Al-husyni
*Daga Group din Tafsir da Jawaban Jagora (H)*
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com