Imam Jafar Assadiq (A.S) |
Makon Imam Jafar Assadiq (As)
WAYE IMAM JAFAR ASSADIQ (AS).
Imam Jafar Assadiq (As) Dane Ga Imam Muhammad Bakir Shi kuma dan Imam Ali Zainul Abidin shi kuma dan Imam Hussain (As) shi kuma dan Imam Ali da Sayyida Fatima Yar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S). Wannan Shine Silsilar Imam Jafar zuwa ga Manzon Rahama Annabi Muhammad (S).
Sunan Mahaifiyar Imam Jafar Assadiq Itace Fatima wacce Akafi sani da umma farwa.
An Haifi Imam Jafar Assadiq (As) Ranar Monday 17 ga Rabi'ul Auwal a shekara ta 83 Hijirar Manzon Allah (S) a Garin Madinatul Munauwara.
Imam Jafar Assadiq Daya daga cikin jerin Limaman shiriya da Manzon Allah yayi mana wasicci da riko dasu a Bayansa, wanda imam jafar Assadiq shine Imami na 6 a cikin Jerin imamai goma 12 da muke dasu tin daga Imam Ali dan Abi Talib zuwa Kan Imam Mahdi (ATF).
Imam Jafar ya Gaji Imamanci ne a wajan Mahaifinsa Imam Muhammad Bakir a Ranar 7 ga Watan Zil-Hijja, 114 H.
Imam Jafar Assadiq yana da yara guda 10 Kamar yanda Sheikhul Mufid ya ambata Wanda Yayan nasa sune kamar haka Ismail, Abdullah,Imam Musa Al-Kazim, Abbas ,Muhammad Dibaj, Ali, Ishak, Fatima,Ummu farwa da kuma Asma'u.
Imam Jafar Assadiq (As) yayi zamani da Sarakuna Kamar haka: Al-Walid bin Yazid bin Abdul-Malik Hisham bin Abdul-Malik, Yazid bin Al Walid bin Abdul-Malik, Ibrahim bin Al-Walid, Marwan Al-Himar, Al Mansur.
Imam Jafar Assadiq Ana Masa Alkunya da Abu Abdullahi, Inda Yake sa Lakuba Kamar haka, Musaddak, Sadik ,Tahir,Muhakkak, Kashiful Haka'ik, Kafil .
AL-Mansur Shi ne Khalifa na biyu a cikin jerin Khalifofin Banul Abbas, kuma ya kasance Mutum ne mai tsananin rowa, ga Karya da Sata, da Zamba da Yaudara, da sauran miyagun halaye da dabi'un da kunne ba zai so ya ji su ba saboda munin su!.
Ya zo a ruwaya daga Ma'aiki (S) yace: "Hakika Jahannama tana da Kofofi bakwai kuma rukunnai ga Fir'aunoni bakwai: Namrud bn Kan'an Fir'aunan Khalil (Annabi Ibrahim as), da Mus'ab bn Walid Fir'aunan Musa, da Abu Jahil bn Hisham, da Wane.. da Wane.. da Yazidu Makashin Dana, da kuma wani Mutum daga Banul Abbas ana yi masa Laqabi da Dawaniqi, Sunanshi Mansur".
Biharul anwar Juzu'i na 30 Shafi na 410.
KADAN DAGA CIKIN MAGANGANUN WASU MALAMAI AKAN IMAM JAFAR ASSADIQ (AS)
1. Al-Imamus-Shafi'i yana cewa:"Shi (Imamu As-Sadiq a.s) yana daga cikin Manyan Ahlul baiti, kuma ma'abucin Ilimi ne mai dimbin yawa, da Ibada cikakkiya, ma'abucin yawan zikiri zartacce, da Zuhudu bayyananne, da yawaita karatun Alkur'ani, yana bibiyar ma'anonin Alkur'ani mai girma, kuma yana fito da Jauharori da abubuwan mamaki daga Koginsa".
A duba Littafin Madalibus-Sa'ul fi Manaqibi Alirrasuli, Shafi na 436.
2. Imamu Malik, Shugaban Mazhabar Malikiyya ya fada dangane da Shi ya ce:"Ido bai taba gani ba, Kunne bai taba ji ba, kuma zuciyar wani Mutum ba ta taba sawwala wani mutum da ya fi Ja'afar bn Muhammad ba, a fagen Ilimi, da Ibada, da Tsantseni".
A wani wajen kuma cewa ya yi: "Idona bai taba ganin wani da ya fi Ja'afar bn Muhammad ba a Falala, da Ilimi da Tsantseni. Kuma ya kasance ba ya wofintuwa daga abubuwa uku: Ko dai yana Azumi, ko yana tsaye yana Sallah, ko yana Zikiri. Kuma ya kasance daga Manyan Gari, Manyan masu Zuhudu masu tsoron Ubangijinsu, kuma ya kasance mai yawan Ilimin Hadisan Manzon Allah (S), mai dadin zamantakewa, mai yawan amfanarwa".
A duba Littafin Manaqibu Ali abi Dalib, Juzu'i na 3 Shafi na 396
3. Hasan bn Ziyad yace: Na ji an tambayi Abu Hanifa Wanne ne mafi ilimin Fiqhu a cikin Malamai?
Sai yace:"Ban taba ganin mafi ilimin Addini ba irin Ja'afar bn Muhammad"
4. Abu Hanifah (Nu'uman) ya yi i'itirafi da cewa da ba domin karatu na shekaru 2 da yayi a wajen Imam as-Sadiq (As) ba da ya Halaka!.
Yana cewa: "Da ba domin Shekaru biyu ba, da Nu'uman ya Hallakka".
Littafin Al-Imamus-Sadiq wal Mazaahibul Arba'ah. Juzu'i na 1 Shafi na 70.
5. Ibnu Hajar Al-Asqalani ya ce:"Ja'afar bn Muhammad bn Ali bn Husain bn Ali bn Ali Dalib, Fakihi ne kuma mai Gaskiya".
A duba Littafin Min Amalil Imamis-Sadik, na Muhammadul Khaliliy, Shafi na 157
6. As-Shahrastaaniy yana fada dangane da Imam jafar Assadiq cewa: "Shi ma'abucin ilimi ne mai tarin yawa a cikin addini, da kuma adabi cikakke a cikin hikima, da zuhudu matuka a cikin duniya, da tsantsani cikakke a cikin Sha'awowi, ya zauna a Madina tsawon zamani yana amfanar da Shi'arsa masu goyon bayan sa, kuma yana fa'idantar da masoyansa asiran Ilmomi, sannan ya shiga Iraqi na wani lokaci, bai taba nuna kwadayin Mulki ba da dai, bai kuma taba jayayya da wani ba a kan shugabanci. Wanda duk ya fada Tekun sanin Allah ba zai yi kwadayin kaiwa Gaaba ba, wanda kuwa duk ya hau qololuwar hakika ba zai ji tsoron fadowa ba".
Littafin Al-Milalu wan-Nihalu, juzu'i na 1 Shafi na 161.
7. Imamu Az-Zahabiy yana cewa: "Ja'afar bn Muhammad bn Ali bn As-Shahid Al-Husain bn Ali bn Ali Dalib al-Haashimiy, Al-Imam Abu Abdillahi al-Alawiy al-Madaniy As-Sadiq yana daga cikin Shuwagabanni kuma zurfin Ilimi".
Littafin Tazkiratul Huffaz na Az-Zahabiy, Juzu'i na 1 Shafi na 157.
8. Al-Jaahiz ya kasance yana cewa: "Jafar bn Muhammad Wanda Iliminsa da Fiqhunsa suka cika duniya!. Kuma an ce Abu Hanifa yana daga Almajiransa, haka ma Sufyan At-Thauriy, kuma iya wadan nan biyun sun wadatar da kai a wannan babin".
Rasaa'ilul Jaahiz, Shafi na 106.
9.. Haka ma Ibnu Hibban an ruwaito yana cewa: Jafar dan Muhammad ya kasance daga Shuwagabannin Ahlul Baiti a fagen Fiqhu da Ilimi da Falala".
Littafin Tahzibut-Tahzib, na Al-Asqalaani Juzu'i na 2 Shafi na 88.
10. Ibn Abi Umair yana cewa:"Na ji Malik Ibn Anas... yana cewa: Imam Sadiq (As) ya kasance mai yawan ruwaito hadisai, mai dadin zama kana kuma wanda ake yawan amfanuwa da shi…"
(Al-Khisal : al-Saduk, b 3, h 219).
Imam Jafar Assadiq (As) Yana da Sahabbai Masu yawa dan haka zamu Ambato kadan daga cikin su. Irinsu Zuraratu bin A'ayan As-Shibaani, Humrasnu bin A'ayan As-Shibaani, Abu Hamzata Ath-Thuhmaali (Thabit bn Dinar), Buraid Bin Mu'auwiya Al-Ajli, Ishaq Bin Ammar Al-Kufiy, Abanu Bn Taglib,Abdullahi bin Abi Ya'afur,Al-Mu'allah bin Khunais, Hisham bn Muhammad bin Sa'ib Al-Kalbi, Muhammad bin Ali bin Nu'uaman Alkufiy da kuma Safwan bin Mihran Al-Jammal Al-Asadi Alkufiy.
Wadannan Sune Sahabban Imam Jafar Assadiq (As)
Maulana Imam Jafar Assadiq (As) Ya Shahara da karamominsa masu Albarka, saboda haka zamu kawo biyu zuwa uku daga cikin karamominsa Masu Albarka.
1. Ya zo a Littafin Basa'irud-Darajaat da Biharul anwar daga Dawud bn Kathir ar-Raqiy yace:Wani Mutum daga cikin Sahabbanmu yayi Hajji sai ya Shiga wajen Abu Abdillahi (As) yace: Ran Babana da Mahaifiyata fansarka ne, hakika Iyalina (Matata) ta rasu, yanzu na wanzu Ni kadai ne!.
Sai Abu Abdillahi (As) yace da Shi: "Kana son ta ne?". Ya ce: Na'am. Sai ya ce da Shi: "Koma Gidanka, za ta dawo Gidan tana cin Abinci".
A lokacin da na dawo daga Hajjin nawa na shiga Gida sai na gan ta a zaune tana cin Abinci!".
Biharul anwar, Juzu'i na 47, Shafi na 81.
2. Haka ma ya zo a Littafin Madinatul Ma'aajizi daga Abus-Saamit al-Halawaniy ya ce: Na ce da As-Sadiq (As) Ka ba Ni wani abu da zai kawar da shakku daga Zuciyata.
Sai Imam (As) yace: "Miko mi Makullin da ke a hannun Rigarka". Sai na mika masa, sai ga Makullin ya zama Zaki!. Sai na tsorata!. Sai ya ce da Ni: Karbi kada ka ji tsoro, sai na karba sai ga shi ya koma Makulli kamar yadda yake!".
Littafin Madiinatul Ma'aajizi Shafi na 416, Hadisi na 236.
3. Ya zo a Littafin Al-Kaafiy cewa: A lokacin da Al-Hasan bn Zaid ke matsayin Gwamna a Makkah da Madina a banka Wuta a gidan Al-Imamu As-Sadiq (As) da umarnin Al-Mansur ad-Dawaniqiy, sai wuta ta kama kofar Gidan da Zauren Gidan, sai Imam (As) ya fito dag a Gidan ta kan Wutar yana taka ta yana cewa: "Ni ne Dan Isma'il (As), Ni ne Dan Ibrahim Khalilullah".
Al-Kaafiy na Sheikh Kulainiy, Juzu'i na 1 Shafi na 473.
WASIYYARSA TA KARSHE A RAYUWARSA:
Ya zo a ruwaya cewa: "Lokacin da Imam As-Sadiq (As) zai cika, ya bude Idanuwansa sannan yace: "Ku tattaro min Makusantana".
A lokacin da suka hadu sai ya kalle su ya ce da Su: "Lallai Cetonmu ba ya kaiwa ga mai wulakanta Sallarsa, bai ba ta muhimmanci ba".
Littafin Mafatihul Jinan Bugun Darul Adwa'i, Bairut, Shafi na 274, a karshe Munasabobin Watan Shawwal.
Imam Jafar (As) ya yi Shahada ne yana da Shekaru 65 a duniya, kuma Dansa Imamu Musal-Kazim (As) ne ya yi masa Wanka, da Hanud (Shafa turaren Al-Kafur a gabobi 7 na Sajjada), da Likkafani, ya kuma yi masa Sallah, sannan ya binne Jikinsa mai Tsarki a Makabartar Baki'a da ke Garin Madinar Manzon Allah (S).
Imam ya bar duniya ne ba tare da ya mallaki komai na daga abin duniya, ya shahara mai a wajan Yada Ilimi kuma Malami Mai gudun duniya mai taimakon gaskiya da adalci, Mai Kira zuwa ga Allah mai yin Alkairi ga mutane tare da shiryar dasu zuwa ga Addini. Mai yin umarni da kyawawa da hani ga munana.
A nan Muka Kawo karshen wannan karamin rubutun da bai wuce koda Cokali guda daya ba, Sannan wannan rubutun kadan ne daga cikin Matsayi da daraja da girma irin na imam Jafar Assadiq (As).
Na Sadaukar ga wannan Rubutun zuwa Ga Mahaifiyata Allah ya kai ladan zuwa Gareta Albarkacin Imam Jafar Assadiq (As).
Amincin Allah Ya Cigaba da Tabbata Agareka ranar da aka Haifeka, zuwa ranar da kayi Shahada da Ranar da za a tashe ka kana Matsayin rayayye.
--Jawad Adamu Tsoho
Asabar 26/11/2022
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com