@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BABU CIGABA GA 'YAR'UWA TA AURI BA'AME
Nazari da fahimtata ne yasa nayi nufin yin rubutu kan wannan take (Title) dake saman rubutuna. Hakan kuwa ya faru ne sakamakon qalu-balantar da wata 'yar'uwa (sister) tayi min kan cewa me yasa dan'uwa (brother) zai iya auren Ba'amiyah amma 'yar'uwa (sister) ba za ta auri Ba'ame ba?
Ba batun haramci ko halasci bane cewa dan'uwa zai iya auren Ba'amiyah, amma 'yar'uwa ba za ta auri Ba'ame ba.
Sayyid Zakzaky (H) yayi gargadi da kwadaitarwa game da auren 'yan'uwa (brothers /sisters) a junansu, wanda samun sabanin hakan cikin 'yan'uwa ba zai zama sabawa wannan magana ta Sayyid (H) ba, domin ba wai umarni yayi cikin wannan magana ba.
Hikimar dake cikin wannan magana tasa ita ce, yin hakan zai iya zama taimakon juna da kuma tsare (restoring) din wannan tarbiyyah da muka samu da fahimta qarqashin koyarwar Ahlul-Bait (A. S) wacce ta zama ita ce haqiqanin karantawar da Annabi Muhammad (S. A. W. W) yayi mana kuma ya barmu a kanta.
Saboda haka idan ya zamana 'yan'uwa (brothers/sisters) na auren junansu zai zama an sami dorewar wannan aqida da koyarwarta ba tare da rushewa ko tabarbarewa ba.
QORAFE-QORAFEN DA AKE SAMU
Daga cikin qorafin da 'yan'uwa (brothers) ke kawowa shine, mafi yawan 'yan'uwa (sisters) na gani kamar matsayinsu ya fi qarfin su auri dan'uwa (brother) marar kudi, kuma abinda ake kashewa wajen aurenta ya fi wanda ake kashewa wajen auren Ba'amiyah. Saboda haka sai su 'yan'uwa maza ke ganin auren wacce ba 'yar'uwa ba ya fi sauqi, kuma an fi mutunta su ko sun fi samun mutuntawa daga wajen wadanda ba 'yan'uwa (sisters) bane.
Ta bangaren 'yan'uwa mata (sisters) da iyayensu kuwa suna ganin lalura ce ke sa su auren Ba'ame saboda sun rasa mazajen aure daga cikin 'yan'uwa (brothers), alhali suna buqatar aure sama da shekaru biyar (5) da isowar matsayin aure amma ba suyi ba sakamakon rashin samu daga cikin 'yan'uwa.
Saboda haka sai su yanke hukuncin cewa duk wanda suka samu daga Amawa matuqar yana da nutsuwa za su iya aurensa a babin lalura.
AUREN BA'AMIYAH
Sanin kowa ne ana samun masu kyawawan tarbiyya cikin kowanne bangare, 'yan'uwa da Amawa kamar yadda ake samun masu munanan tarbiyya daga kowanne bangare. Sannan kuma idan aka dubi 70% na 'yan'uwa mata (sisters) da suka haura shekaru hamsin (50) a duniya komai qoqarinsu cikin wannan harka za ka samu an auro su ne a matsayin Amawa ko ma ace su 'yan'uwa maza (brothers) nasu a matsayinsu na Amawa su kayi aure, amma yanzu sun zama ababen kallo ayi koyi dasu cikin wannan harka.
Saboda haka idan ka auri Ba'amiyah ta zama 'yar'uwa ta sanadinka haqiqa ka yi Jihadi wanda Allah ne kadai yasan girman ladan da za ka samu. Dogarona na wannan magana shine fadin Manzon Allah (S. A. W. W) ga Imam Ali (A. S) cewa :
" DA ACE MUTUM 'DAYA ZAI SHIRYU TA HANYARKA YA FI ALJHAIRI GARE KA FIYE DA A BAKA GARKEN JAJAYEN RAQUMA.
Na san babu wanda ya isa yace ka auro Ba'amiyah ta zama 'yar'uwa (sister) ta hanyarka ya ci karo da wannan magana ta Sayyid (H).
Da yawa ana samun masu fahimtar harka amma suna wani irin guri ne na lungu ko Qauye inda babu 'yan'uwa mata a gurin, kuma ba zai sami 'yar'uwa daga maraya (town/city) ta aminta ta shigo da nufin rayuwa a wannan guri ba, amma shi zai iya auren wata daga qauyen nasu wacce ba 'yar'uwa ba ya riqa shiga da ita guraren da ake harka har ta dabi'antu da koyarwar harka.
AUREN BA'AME
Babu kokonto yadda miji ke da tasiri kan mace musamman bayan aure a daidai lokacin suna cikin tsananin soyayya ya juyata yadda yake so, amma abune mawuyaci ace mata ta canza miji zuwa kan wata aqida tata sabanin wacce yake kanta kuma yake ganin ita ce daidai.
Saboda haka idan aka ce 'yar'uwa ta auri Ba'ame haqiqa ta nisanta da harka imma ba ta zama tana adawa da ita bayan nisan zama ba. Ba zai taba yiwuwa ace miji na matsayin Basalafe ko Ba'izale ace yana barin matarsa na zuwa guraren tarukan na 'yan'uwa ba, kenan idan ta aure shi ta samu ci-baya ne a addininta ba cigaba ba.
Zaiyi wuya ace cikin 'yan'uwa mata 30 su auri Amawa sannan a sami 10 daga cikinsu su fahinci harka ta sanadinsu, domin za kaga da yawa wasu Amawa na kusantar 'yan'uwa saboda suna neman wasu daga 'ya'yensu da aure, amma idan basu samu ba sai su juya baya.
Wannan abu kuwa yayi kama da wadanda su kayi Hijrah zuwa Madinah domin mata ba wai don Annabi (S. A. W. W) ba.
YAA ALLAH KA TAUSAYA MANA KA BAWA 'YA'YAYENMU MATA 'YAN'UWA NA GARI DON CETON IMANINSU DA SAMUN RABAUTARSU
🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah.
(08137925034)
14th November, 2022/ 20th Rabi'us-Sani, 1444.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com